Ba Zamu Yarda Da Yunkurin Cin Zarafin Osinbajo Ba – Matasan Nijeriya

Daga Wakilinmu

Kungiyar matasan Nijeriya ta fito fili ta bayyana goyon baya gami da yabawa da salon shugabanci da dattaku na mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sannan Ƙungiyar ta tabbatar da cewa ko da wasa ba zata amince da wani yunkuri na cin zarafin shi ba.

Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna Shugaban Ƙungiyar Matasan Nijeriya Honorabul Abdullahi Abubakar Wali, yace matasan Najeriya sun damu sosai dangane da rashin kunya da cin mutunci da Timi Frank ya yi wa mataimakin shugaban kasar, inda ya zarge shi da danne wasu kudade, zargin da bai da tushe ballantana makama, illa kawai shaci fadi da rashin kunya da Timi Frank ke da shi, domin wata manufa ta bata darajar mutum mai dattaku irin Osinbajo.

Matasan Najeriyan sun ce suna goyon baya ga matakan shari’a da Osinbajo yace zai dauka akan wannan cin zarafin da akayi mishi, wanda Timi Frank da sauran ‘yan barandar shi suka yi mishi.

Kungiyar matasan Najeriya sun fallasa cewar akwai siyasa a cikin yarfen da Timi Frank ya yi wa Osinbajo, domin ga dukkanin wanda ya san Timi Frank ya san da cewar shi daya ne daga cikin yaran Atiku Abubakar, saboda haka maganar shi abin yin watsi da fatali da ita ne

Leave a comment