SHEKARU HUDUN GWAMNATIN EL-RUFA’I: Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu-  Yaro Maikyau

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Dan majalisar dokokin Jihar kaduna mai wakiltar Al’ummar mazabar Unguwar Sunusi, Honarabul Auwal Muhammed Yaro Maikyau, ya bayyana nasarar da Shugaban kasa, Gwamnan Jihar kaduna Malam Nasiru Ahmed El-rufai da kuma Sanata mai wakiltar Al’ummar kaduna ta Tsakiya Sanata Uba Sani, suka samu a kotun sauraren korafe korafen zabe da ya gabata, da cewa hakika wannan nasarar ba komai ya janyo ta ba illa gaskiya da rikon amana irin na jam’iyyar APC.

Honarabul Auwal Yaro Maikyau, ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da wakilinmu na tsawon mintuna goma 15, dangane da irin nasarar da ‘ya’yan jam’iyyar APC musamman Shugaban kasa Muhammad Buhari, Gwamnan Jihar kaduna, Malam Nasiru Elrufai, da kuma Sanata Uba Sani, suka samu a kotunan sauraren korafe korafen zabe da ya gudana a fadin kasar nan baki daya.

Yaro Maikyau ya kara da bayyana cewa, ” Idan kayi la’akari da irin dimbin ayyukan ci gaban kasar nan da Shugaban kasa Muhammad Buhari karkashin jam’iyyar APC, ya kawo ma daukacin Al’ummar dake sassa daban daban na fadin kasar nan, tabbas idan akayi la’akari da hakan kasan ba wani abin mamaki bane don ance ya sake lashe zabe a karo na biyu. Domin ayyukan da Shugaba Buhari ya gudanar kawai a zango na farko sun isa Al’ummar kasar nan su sake zabensa domin ya sake Shugabancinsu a zagaye na biyu.

Da kuma ya juya kan batun nasarar da Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Elrufai, ya samu a kotu. Honarabul Auwal Muhammad Yaro Maikyau, cewa ya yi, ” Ai wannan ba abin mamaki bane, domin a ranar zabe tun kamin karfe 12 na rana tuni jama’ar Jihar kaduna suka fito kwansu da kwarkwatarsu suka sake zaben Malam Nasiru Elrufai domin ya sake dawowa a zage na biyu, domin Al’ummar Jihar kaduna Maza da Mata sun yi ittikafin cewa, Malam katafila ne sarkin aiki, saboda ina tunani tun bayan wucewar su Margayi Sardauna, babu wani gwamna daya tilo da ya kama kafar yin aiki irin na Mai girma Malam Nasiru Elrufai, saboda gaba daya Birni da kauye babu inda ayyukan alherinsa basuje ba, musamman idan ka dauki fannin sha’anin tsaro, inganta kiwon lafiya, samar da ingantaccen ilimi, gina hanyoyi, samar da ayyukan yi ga Matasa, bana tunanin duk fadin jihohin kasar nan za’a sami wani gwamna tamkarsa, hatta su kansu gwamnoni takwarorinsa sukan fadin haka, dalilin da yasa kenan suke masa lakabi da limamin Gwamnonin Nijeriya.”

“A bangare daya kuma, shi Sanata Uba Sani, kowa yasan mutum ne jajirtacce, wanda ya bada muhimmiyar gudunmuwa wajen ci gaban jam’iyyar APC da kuma siyasar Jihar kaduna. Sannan daga zuwansa majalisa har ya gabatar da wasu kudirori wanda zai kawo ma Al’ummar mazabarsa da kuma Jihar kaduna ci gaba, wanda yin haka ba karamin abin a yaba masa ba ne.”

Da kuma aka tambaye shi, shin ko me zaice game da fatan alheri da yake samu a kullum daga dimbin Al’ummar mazabarsa dangane da irin taimkon da yake basu? Honarabul Auwal Muhammad Yaro Maikyau, cewa ya yi,” ai jama’a rahama ne, domin su suka kawo mu kan matsayin da muke a yanzu, saboda ba domin su ba, da bamu zo inda muke a yanzu ba.”

“Kuma ni burina a kullum bai wuce na ganin ina tallafa ma Al’ummarmu ba, dai dai da abin da zamu iya, wanda kuma yafi karfinmu sai mu basu hakuri, domin da bazarsu muke rawa. Kuma Insha Allahu kamar yadda muka bayyana ne a baya, zamu yi bakin kokarinmu na ganin mun ci gaba da tallafa masu dai dai gwargwadon karfinmu.” A cewarsa.

Leave a comment