TAKADDAMA: Ni Na Kai Kaina Ofishin EFCC- Shehu Sani

Sanata Shehu Sani tsohon dan majalisar dattawa ya kai kansa hukumar EFCC inda ya shafe lokaci yana amsa tambayoyi kan wata huldar da ta shafi cinikin mota.

Mai taimakawa sanatan kan harakokin siyasa Suleiman Ahmad, ya shaida wa BBC cewa Shehu Sani ya kai kansa ne EFCC tun kafin ranar Alhamis da aka bukaci ya gabatar da kansa.

Ya ce wani dan kasuwar sayar da motoci ne ya shigar da kara EFCC game da cikon kudin wata mota da suka yi ciniki.

Sai dai babu wani cikakken bayani daga EFCC kan dalilin gayyar Sanatan.

Amma a cewar Suleiman Ahmad mai taimaka masa, shugaban kamfanin sayar da motci na ASD ne ya yi wa Sanatan tayin mota sabuwar yayi kirar Peugeot 508 don ya musanya masa da Peugeot dinsa da aka daina yayinta.

“Sanatan ya amince amma ya nemi ya biya a hankali, kuma ya amince akan farashin miliyan 17 da dubu dari biyar.”

“Sanata Shehu Sani ya dauko dala dubu 12 ya ba shi da farko, daga baya kuma ya sake ba shi wasu kudin dala dubu ashirin da biyar,” in ji shi.

Image captionTakardar shaidar ciniki tsakanin Shehu Sani da ASD motors

Ya ce ya yi mamakin yadda aka ce shugaban kamfanin na ASD wanda suruki ne ga Sanata Shehu Sani ya shigar da kara a EFCC bayan sun yi magana zai cika masa kudinsa.

Ya kuma musanta zargin da ake cewa Shehu Sani ya zambaci mai kamfanin motocin ASD Motors.

Sanata Shehu Sani ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019.

Leave a comment