Ni Na Kawo Cutar Korona Jihar Kaduna- El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmed El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa shine ya kawo cutar korona a jihar Wanda yanzu ta Yadu a sassa daban-daban a jihar.

Gwamna El-Rufa’i, yace ya dauko cutar ne daga Birnin Tarayya Abuja Wanda ya gogawa mutane hudu da suke aiki tare fashi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a Wani zantawa da kafafen gidajen rediyon da suke jihar suka zanta da shi, inda yace Gwamnatinsa tana dauka matakan da suka kamata wajen dakile yaduwar cutar korona a fadin jihar Baki daya.
Da yake bayani dangane da yadda Cutar Korona ke Kara yaduwa a jihar, yace ” baya ga Ni da na kawo cutar korona jihar kaduna; na Kuma gogawa mutane hudu da suke aiki tare da, Duk sauran wadanda suka kamu da cutar matafiya be daga Jihohin Kano da Legas da wasu jihohi wadanda suka shigo cikin jihar Kaduna.
Akan Dokar Hana fita a jihar, gwamnan ya Kara da cewa ” kamar yadda suke damuwa da Zaman gida muma abin ya shafe mu, hasalima, Zaman gida shine mafita wajen dakile yaduwar cutar a jihar”

Leave a comment