Majalisar Dattawa Ta Nemi Sake Nazari Kan Kayyade Shekarun Daukar Aiki

Majalisar Dattawan Nijeriya ta bukaci ma’aikatar kwadago da nagartar aiki da ta kafa kwamitin da zai sake yin nazari akan tsarin kayyade shekaru wajen daukar aiki, domin bai wa matasa da suka kammala karatu damar samun ayyukan yi.

Bukatar hakan kunshe ne a cikin wani kudiri da Sanata Ibrahim Gobir daga jihar Sokoto, ya gabatar a zaman Majalisar na ranar laraba.

Wakilin Muryar Najeriya a Majalisar Dokoki, Abdulkarim Rabiu, ya rawaito cewa, Sanata Ibrahim Gobir ya ce akwai bukutar sake yin nazari akan yadda hukumomin gwamnati da kanfanoni masu zaman kansu suke kayyade shekaru na daukar ma’aikata, wanda hakan ke sa wa da dama daga cikin wadanda suke da takardun kammala karatu ba sa samun guraben aiki.

Ya ce sakamakon karuwar rashin ayyukan yi a Najeriya, da yawa daga cikin matasan da suka kammala karatun digiri , sun Kan shafe shekaru kusan goma suna neman aiki, wanda hakan ke kawo koma baya a ci gaban rayuwarsu.

“za ka ga mutane da dama suna rage shekarunsu domin su yi daidai da shekarun da aka kayyade na daukar aiki.” In ji Sanata Gobir

Kazakila ya ce abin takaici ne yadda rashin aikin yi ke sanya wasu shiga ayyuka na aikata laifi wanda hakan ke Kara haifar da aikata laifuka da rashin tsaro a cikin kasar.

Daga karshe Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta umarci Ma’aikatar kwadago da nagartar aiki da ta kafa kwamitin da zai sake yin nazari akan tsarin kayyade shekarun daukar aiki.

Leave a comment