Mun Gajji Da Zaman Dirshen A Gida, A Bude Mana Makarantu- Kungiyar NANS

Kungiyar Dalibai ta Nijeriya National Association of Nigerian Students (NANS) ta bukaci gwamnatin kasar data gaggauta bude makarantu.

Babban sakataren kungiyar mai kula da rukunin A Comrade Abdullahi Muhammad Saleh ya bayyana haka yayin ganawar sa da manema labarai a cibiyar yan jaridu ta NUJ dake jihar Kano arewa maso yammacin Najeriya.

Abdullahi Saleh yace ci gaba da zaman gida da dalibai ke yi na jefa rayuwar da dama daga cikin su cikin hadari. Cikin tattaunawa da suka gudanar a baya da manema labarai sun bayyanawa gwamnatin irin illolin dake tattare da hakan.

A cewar sa akwai kasashen da illar da cutar Covid 19 da aka fi sani da Corona Virus tayi musu ta ninninka ta Najeriya, amma duk da haka sun bude makarantun su, saboda haka suke kira da babbar murya ga gwamnatin data ceto rayuwar matasa da yaran kasar.

Bugu da kari, sakataren kungiyar na rukunin A ya bayyana karin dalilan da suka tilasta musu ci gaba da wannan raji a dai dai da wannan lokacin:

” Dalili kuwa shi ne an bude kusan dukkanin abubuwan da ake mu’amulla da su kamar irin su kasuwanni, wuraren cin abinci, shakatawa da wasanni. Wanda kuma muna da yakinin a makaranta ba a cinkoso kamar yadda ake yi a wannan wuraren.

” Sannan kuma makarantu sunyi shiri sosai da sosai wajen yaki da wannan cuta, kusan a nan jihar kano makarantu irin su Jami’ar Bayero, kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi kano Poly duk sun samar da man wanke hannu da takunkumin fuska”.

A cewar wannan kungiyar lamarin cutar Covid 19 musiba ce da ta shafi duniya baki daya, saboda haka dole a zauna domin zakulo maslahar da zata magance ce mana ita a cikin gida, tsoron da muke yi shi ne ana cinye lokaci mai matukar muhimmanci a rayuwar mu, mu kuma muna garkame a gida.

Ganin cewa wannan kungiya a baya tayi barazanar yin zanga zanga domin nuna rashin jin dadin su kan kin bude makarantu ko yaya wannan mataki yake kawo yanzu? Sai Abdullahi Saleh yace:

“Kamar yadda na fada, tun a baya anyi yunkurin zanga zanga, amma mun yita hakurkurtar da dalibai su jinkirta wannan tsari na zanga zanga.

“Hakan kuwa na faruwa ne saboda halin da kasar mu ke ciki na rikice rikice a sassan kasar, idan muka ce zamu yi to za a iya samun wata kafa da za a iya samun wata matsala. Amma nan zuwa wani lokaci zamu ci gaba da bibiya har zuwa lokacin da gwamnatin ta bude makarantun”.

Daga bisani babban sakataren kungiyar mai kula da rukunin A Comrade Abdullahi Muhammad Saleh ya bukaci daliban da su ci gaba da hakuri domin suna da yakinin hakar su zata cimma ruwa nan bada jimawa ba.

Rukunin A na wannan kungiyar dalibai ta NANS dai ta hada da jihohin Kano, kaduna, Katsina, Jigawa, zamfara, Sokoto da Kebbi. Sauran sun hada da Bauchi, Gombe da Niger

Leave a comment