‘Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Malaman Makaranta A Birnin Gwari

Daga Shehu Yahaya, kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar Da cewa ‘yan bindiga Sunyi Garkuwa da Malaman makarantar firamare mallakar gwamnatin jihar a karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan ma’aikatar tsaro da lamuran cikin gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan a taron manema labarai da Yayi a jiya litinin a sakatariyar kungiyar ‘yan jaridu ta jihar Kaduna.
Kwamishinan ya ce “yan bindiga sun kai hari ne da safiyar ranar litinin a garin Rima dake cikin karamar hukumar Birnin Gwari inda suka samu nasarar awon gaba da Malaman.
Yace babu wani Dalibi da aka sace illa wasu guda Biyu sun guda amma daga bisani an gansu.
Aruwan yace Malam da aka sace sune Rabi’u Salisu da Bala Sani da kuma Aminu Habibu Wanda yanzu haka suna hannun ‘yan bindigar.
Aruwan ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta dukufa wajen daukar Matakan tsaro wajen ceto Daliban jihar Kaduna.

Leave a comment