‘Yan Nijeriya Sunyi Murna Da Sake Bude Iyakokin Kan Tudu

Kwantirola Joseph Attah ke bude iyakar Kamba

Daga Shehu Yahaya

Mazauna garuruwan da ke kan iyakokin Najeriya da aka rufe na ci gaba da bayyana farin-cikinsu bayan da hukumomin ƙasar a hukumance suka buɗe iyakokin da ke kan tudu a ranar Litinin.

Hukumar hana fasa-ƙwauri ta ce gwamnatin tarayya ce ta ba da umarnin buɗe iyakokin huɗu a ƙarshen makon jiya.

An dai amince a bude iyakokin Idoroko a jihar Ogun da Jibiya dake jihar Katsina sai kuma iyakar Kamba a Kebbi da kuma iyakar Ikom a jihar Cross River.

Bayan bude iyakar Jibiya a Katsina, mutanen da ke yankin sun bayyana jin dadinsu kasancewar harkokin kasuwanci zai farfado a cewarsu.

Alhaji Salisu O I Jibiya, ya shaida wa BBC cewa, bude iyakokin nan ya sanya su cikin jin dadi da raha saboda sun shafe shekaru uku suna rufe abin da ya sanya su cikin takura.

Ya ce, duk da ka’idojin da hukumomi suka gindaya musu na irin abubuwan da za a rinka safararsu ta iyakokin, su kam sai san barka saboda koba komai za su ci gaba da kasuwancinsu da suka jima basa yi.

Alhaji Salisu O I Jibiya, ya ce ” A yanzu an yarda mu shigo da abubuwa da suka hada da wake da aya da kuma dabino, amma duk sai mun biya kudin fito.”

To amma ba suce mu biya kudin fito a kan kayan abinci kamar shinkafa da taliya da cous cous da dai makamantansu ba, in ji shi.

Ya ce, duk wadannan sharadai su kam ba su damu ba domin ba bu wani alfanu da rufe iyakokin ya kawo musu sai bakar wahala da suka sha

jihar Kebbi ma, an bude iyakar Kamba, inda al’ummar garin suka shaida cewa suna cikin farin ciki marar misaltuwa saboda abin da suka jima suna jira ne ya faru.

Yahuza Sahabi, mazaunin garin Kamba ne inda aka bude iyakar, ya kuma shaida wa BBC cewa, bude iyakar nan shi ne babban alfanu garesu, domin za su samu saukin farashin kayayyaki musamman na abinci.

Ya ce,” A gaskiya mu mutanen da ke rayuwa a garuruwan da ke kan iyaka, rufe su ya yi matukar taba mana rayuwa musamman ta fuskar tattalin arziki.”

Yahuza Sahabi, ya ce a lokacin da aka rufe iyakarsu sun ga kalubale kala-kala, saboda yadda farashin kayan abinci ya tashi sosai, ba karamin kuncin rayuwa muka shiga ba inji shi.

Ya ce, amma a yanzu tunda an bude iyakar, farashin kayan abinci da ma sauran kayan bukatun yau da kullum zai sauko.

Leave a comment