From Ibraheem Hamza Muhammad
Sanata Kashim Shettima ya jaddada cewa ‘kasar Najeriya zata mori romon mulkin dimokradiya idan aka zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin Shugaban ‘Kasa a zaben da ke gabatowa.
A takardar sanarwa da kakakin kwamitin APC mai neman a za’bi Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima, Mista Bayo Onanuga ya fitar, ta ce, Sanatan ya furta haka ne a ranar Litini a Legas yayin da ya wakilci Tinubu a taron shekara-shekara na Kungiyar Lauyoyi ta kasa. Inda ya ce, aikin gani-da-ido da Tinubu da Shettima suka aiwatar a Lagos da Borno ya zama manuniyar cewa su masu aiki tukuru ne.
Tsohon Gwamnan na Borno ya ce, duk da yanayin rashin tsaro a Arewa-Maso-Yamma yayin da yake mulki, ya taka rawar gani a fannin ilmi.
Sanata Shettima ya kara da cewa, “Jama’a suna da alhakin su yabawa mai aiki a maimakon mai yawan dogon turaci.
” Ya dace Jama’a su bi wanda ya san hanyar zuwa ga daukaka, domin in an zabe mu, a ranar farko za mu fara aikin yalwata tattalin arzikin kasa, samar da yanayi mai alfanu da kuna inganta tsaro.
“ Da Tinubu da ni gwaraza ne da muke son gina ‘kasa: Alal misali, ana iya zuwa Borno don gani-da-ido yadda na gina makarantu, sannan na inganta samar da ilmi gadan-gadan duk da ana yaki da masu dauke da makamai a lokacin.
” Ba za mu yi ‘kasa a gwuiwa ba wajen kambana ayyukan da muka yi a jihohinmu don ciyar da jama’a su sami bunkasa.” .
” A takaicen-takaitawa, mun kuduri aniyar yin jagoranci na gari. ” A cewar Sanata Kashim Shettima.