Honorabul Babawo Ya Kaddamar Da Gina Dam Na Noman Rani

Daga Idris Umar Zariya

A cikin makon daya gabata ne Dan majalisa taraiyya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari Honorabul Garba Datti Babawo ya kaddamar da gina Dam a garin Sakadadi cikin karamar hukumar ta Sabon Gari Jihar Kaduna.

A lokacin kaddamar da wannan (Dam ) din Dan majalisa yace wannan (Dam) jama’ar Najeriya ne zasu amfana dashi ba jama’ar karamar hukumar Sabon Gari ba kadai

Ya kuma kara da cewa samun nasaran gina wannan (Dam) ya zama daya daga cikin abin jin dadinsa a gaba daya rayuwarsa ta siyasa domin hanyace ta samun lada zuwa ga Allah mahallci.

Don haka ya tabbatar da cewa wannan aikin zai lashe kudi a kalla Naira Miliyan dari biyar.

Kuma aikin gina Dam din yana karkashin hukumar gina Dam na Upper Niger Rever vexing Autoroty ne

Shima Shugaban Karamar Hukumar Sabon Gari Honorabul Enjiniya Ibrahim Usman yayi godiyane ga Dan majalisar bisa nuna kwazo tare da nuna kishi da yake wa jama’ar karamar hukumar ta Sabon Gari.

Yace banda harkar bukasa tattalin arzukin kasa wato kawo hanyar bukasa noma ya taba bangarori da dama kamar bangaren lafiya da bangaten Imlin zamani.

Don haka ya sha alwashi marawa Dan majalisar baya don samun damar karike abubuwan da ya faro a gabansa ya kuma yi godiya a madadin shi kanshi da jama’ar karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna baki daya.

Shima injiniyan Garba Muhammad Lawal wanda aikin gina (Dam ) din ke hannunsa ya sha alwashin bin duk ka’idojin da aka bashi kuma ya taya jama’ar karamar hukumar Sabon Gari murna samun gina wannan (Dam) mafi giram a cikin dukkan (Dama- Daman) da suka gina a wannan gwamnatin.

Karshe yayi kira ga jama’ar karamar hukumar Sabon Gari da su basu goyan baya yayin gudanar da aikin nasu.

Leave a comment