Yadda Likita a asibitin Aminu Kano ya ‘rubar’ da hannun jariri dan kwanaki uku a duniya

Daga Hydar Usman

Ana zargin wani likita a asibitin koyarwa na Aminu Kano da illata wani jariri ɗan kawanaki biyar.

Likitan dai ya bar tsirkiyar da ya ɗaure hannun jariri da ita yayin daukar jini har tsawon awanni 18.

Wanna ne ma ya jawo hannun yaro ke neman rubewa a halin yanzu

Gidan Radiyon premier ta ce an yiwa mahaifiyar yaro aikine aka ciro shi daga cikinta.

Daga bisani likita ya ce yana fama da matsalar numfashi da hakan ta sa tilas aka kwantar dashi a bangare jarirai.

an kuma yi zargin cewa, awa 18 ba wani daga cikin jami’an lafiya a asibitin da ya kula yaron, balle ya lura da ɗaurin dake hannunsa, har sai da mahaifiyarsa taje bashi mama.

Tuni dai wasu likitoci suka ce sai dai a yanke hannun wanna jariri, sakamakon shafe tsahon lokaci jini bai gindaya ba.

Sai dai mahaifin yaron Malam Umaru Shamsu ya ce ma’aikatan asibitin na nuna masa wulakanci duk da dattakon da ya nuna.

Ya ce ya yi mamaki da aka kirashi wai yaje ya siyo maganin da za a baiwa ɗan nasa a ranar Litinin, duk da ɗanyen aikin da aka yi masa.

A Talatar nan 3 ga Janairu yaron ke cika kwanaki 5 da haihuwa.

Leave a comment