An Baiwa Almajiran El-Zakzaky Ababen Hawansu da Hukuma Ta Kama A Zariya

Daga Idris Umar,Zariya

Shekaru bakwai da samun takaddama tsakanin mabiya mazhabar Shi’a da ake kira almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky anfi sanin su da ‘yan shi’a.

fiye da mutum dubu daya ne ake zargin sun rasa ransu a lokacin tataburzan na shekaran Disambar 2015, a yayin wannan rashin fahimintar.
An tsare ababen hawa masu yawa da suka hada da motoci da babura bayan tsawan lokaci ne kotu ta bayar da umurni a ba almajiran shehin kayansu.

A ranar Asabar 1 ga watan Afrilun 2023 aka bai wa mabiya mazhabar shi’ar motocinsu da baburansu da Keke Napep bayan da wata babbar kotu a Kaduna ta bada umurnin hakan bayan kwashe tsawon lokaci ana tafka shari’a.

Sai dai da yawan motocin an farfasa su da harsasai. A yayin da wasu motocin da aka damkawa ‘yan sanda ajiyarsu an samesu babu injinansu da batiransu da tayoyinsu da rima-rimansu da dai sauran su.
Barista M. Abu, lauyan dake wakiltar ‘yan shi’ar a yayin ganawa da manema labarai cikin harshen Ingilishi, ya bayyana cewa; sun zo ofishin ‘yan sanda na MTD ne bisa hukuncin kotu da suka samo a madadin wadanda suka shigar da kara; “wato Harkar Musulunci a Nijeriya wadanda aka fi sani da ‘yan Shi’a. Mun samu hukuncin kotu kan a sakar musu ababen hawansu daga babbar kotun Kaduna. Mun zo nan ne domin tabbatar da an bi wannan hukuncin”, inji shi.

Da yake karin haske, Barista M. Abu daya daga cikin lauyoyin da suke kare mabiya mashabar ta Shi’ar ya ce; “adadin ababen hawan da muka shigar da kara a kai ya kamata ya zarce adadin wadanda muka gani yanzu a nan.

Ababen hawan da ke kasa a nan guda 67 ne kawai. Kuma yakamata a ce sun fi haka. Ko wadanda muka gani a nan duk an lalata su. Bai kamata mu same su a wannan yanayin ba”, ya lurantar.

Lauyan da ya tsayawa ‘yan shi’ar a kotu ya ce bayan abin da ya faru tsakanin ‘yan shi’a da sojoji a Disambar 2015, an kama daruruwan ‘yan shi’a bisa zargin tare hanya tare da ababen hawansu; “wadanda mafi yawa aka kwashe a gefen hanya da kuma gidan Malaminsu, Malam El-Zakzaky. Inda sojoji suka tattare musu ababen hawansu tare da kama mutane wanda suka mikawa rundunar ‘yan sanda domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su domin yanke musu hukunci. An tafka shari’a wanda a karshe dukkanin wadanda aka kama aka sake su tare da wanke su daga dukkanin zarge-zarge”.

Ya kara da cewa; “amma a bangaren ababen hawansu wadanda aka ajiye a MTD, kuma ba a taba gabatar da su a gaban kotu ba a lokacin shari’a. Bayan wancan hukuncin mun dauki matakin ganin an bayar da ababen hawan amma hakan ya cutura saboda wasu dalilai nasu Dole ta sa muka shigar da kara kan hakan. Sakamakon hukuncin da kotu ta yanke cewa a bayar da ababen hawan ne ya sa muka kasance a nan a yau”

Lauyan ya ce tun cikin shekarar 2022 kotun a karkashin mai shari’a A. A Amina ta bayar da umurin bayar da ababen hawan. “daga lokacin da kotun ta bayar da umurni zuwa yanzu ya dauki lokaci”, inji shi.

Lauyan ya tabbatar da cewa; za su duba matakin da za su dauka a gaba duba da cewa ababen hawan da aka ba su ba su kai wadanda suka shigar da kara suna nemaba.
.

A yayin zantawarsa da ‘yan jarida, daya daga cikin wadanda suka rasa abin hawansu, Malam Sidi Muhammad Rabiu mazaunin garin Kaduna, ya ce; “kayayyakin kamar yadda muka zo muka same su da yawansu an ciccire abubuwan da suke cikin Babura da motoci, an cire injinansu. Mafi yawan kayayyakin sai dai ka dauki gwangwanin mota ko babur. Kamar ni babur dina ma an cire tayoyin ne ma”, in ji shi.

Injiniya Ahmad Gilima, daya daga cikin wanda ya zo karbar motarsa, ya ce; bayar da ababen hawan ya sake nuna irin abin da ya faru a lokacin da abun ya faru musamman a wannan lokacin

Wakilinmu ya labarto cewa; mafi yawan masu ababen hawan da aka bai wa kayansu lamarin ya rutsa da su ne a muhallan da suke gabatar da taronsu wato Husainiyyah Bakiyyatullahi da kuma Gidan Shaikh Zakzaky dake Gyallesu.

Wakilinmu da ya halarci wurin bayar da ababen hawan ya tarar da ‘yan Shi’ar da dama ne suka hallara a ofishin ‘yan sandan dake lura da tattara ababen hawa na MTD dake karamar Hukumar Sabon Gari a Zariya domin bayar da shaidar abin hawansu domin su dauka. Inda suke cike wani takarda dauke da sa hannun Lauya kafin ba su abin hawansu.

Daga cikin ababen hawan akwai motocin lafiya na agajin gaggawa mallakin cibiyar lafiya karkashin shugabansu Shirk Ibrahim El-Zakzaky wato ‘ISMA Medical Care Initiatives’ duk an kamasune a shekarar Disambar 2015 bayan sun masu amfani da motar an nemesu ba a gansuba har zuwa wannan rana da za a karbi motar.

Malam Sahifah, dayane daga cikin wadanda suka bibiyi tabbatar da ganin an bayar da ababen hawan, ya tabbatar mana da cewa; sun karbi motoci 67, babura 10, Keke Napep guda uku.

Rahotanni sun labarto cewa a cikin watan Disambar 2015 ne sojoji suka dira kan mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a bisa zargin tare wa shugaban Hafsan sojoji na wancan lokaci, Laftanar Janar Tukur Bururai hanya a Zariya. Lamarin da ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi.

Bincike ya nuna cewa bayan an sami sabani da sojoji ne da sun ‘yan shi’ar ne aka sami tabbacin an sami rasa rayuka da yawa ta bangaren jihar da lamarin ya faru wato jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da bizne mutum 347 a ramin bai daya, a yayin da bangaren almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka misanta hakan

A lokacin Kungiyoyin kare hakkin Bil’adama na Amnesty International da Human Rights Watch sun ce wadanda aka kashe sun fi adadin da gwamnati ta ayyana amma bicike ne zai iya bayar da tabbacin.

Ya zuwa hada wannan rahoton komi na tafiya kamar yadda kutu ta bayar da umurni .

Leave a comment