An haramtawa limamai karanta Qur’ani daga wayar hannu a lokacin Tarawi da Tahajjud

Ma’aikatar kula da harkokin addinin Musulunci da wakafi ta kasar Kuwait ta bayyana haramta wa limamai karanta Alƙur’ani daga wayoyinsu na hannu a lokutan sallolin nafilfilun dare na watan Ramadana.

Jaridar Al-Rai ta ruwaito cewa hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta samu sa hannun ƙaramin minista mai kula da harkar masallatai, Salah Al Shilahi.

Sanarwar ta ƙarfafa wa limamai gwiwa da su riƙa amfani da haddarsu ta Ƙur’ani a lokutan sallolin Tarawihi da Tahajjud, kasancewar su (limaman) misali ne ga sauran al’umma.

Ta ƙara da cewa ya kamata kowane limami ya yi muraji’ar karatunsa yadda ya kamata gabanin jan sallah a maimakon karantowa daga cikin waya

Leave a comment