Sarkin Kano Ya Jagoranci Sallar Jana’izar Wazirin Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jagoranci Sallar Jana’zar Marigayi Limamin Waje Wazirin Kano Murabus Sheikh Nisir Muhammad Nasir.

An dai gudanar da Sallar Jana’zar ne da Karfe 9:00am na safiyar ranar Alhamis dinnan ne a Kofar Kudu fadar Mai Martaba Sarkin Kano.

Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero yana daga cikin manyan mutane da suka halarci Jana’zar, da sauran manyan Mutane da Shehunnai da limamai da Yan Kasuwa da sauran al’uma.

Bayan idar da Sallar Jana’zar ne Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da Dan uwansa Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da sauran daruruwan al’uma aka tafi rakiyar gawar Marigayin.

An dai binne marigayi Sheikh Nisir Muhammad Nasir ne a Makabartar Dan Dolo dake Gordon Dutse cikin yankin Karamar Hukumar Gwale dake Birnin Kano.

Mai Martaba Sarkin yayi addu’ar Allah ya gafarta masa yasa aljanna makoma a gareshi tareda baiwa iyalai da “Yan uwa da sauran al’uma hakurin jure rashin Wazirin Kano Murabus kuma Limamin Waje Sheikh Nisir Muhammad Nasir.

Kafin rasuwarsa Sheikh Nisir Muhammad Nasir babban Amini ne ga marigayi Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayero Wanda ya bayar da gudunmawa a bangaroei daban daban ta hanyar cusa kyawawan dabi’u ga matasa da cusa musu soyayyar Annabi Muhammadu SAW.

Sheikh Nisir Muhammad Nasir ya rasu yabar matansa na aure da Yaya da kuma jikoki masu yawa.

Leave a comment