SADAKA JARIYA FOUNDATION ta kara horar da manoma 50 a karamar bukumar kudan

Daga Idris Umar,Zariya

Sadaka Jariya foundation karkashin jagorancin shugabanta honorabul Dauda Iliya ta kara shirya taron karawa juna sani game da sanin aikin gona a zamanance musamman ga manoman karamar hukumar kudan dake jihar Kaduna.

Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafen yada labarai da suka halacci taron.

Taron an gudanar dashine a bubban dakin taro na garin hunkkuyi.

Kuma ya sami karbuwa ta bangaren sarakuna da limamai da manoma daga dukkan fadin karamar hukumar ta kudan.

Farfesa Hamza Mani Shine bubban jami’i da ya bayar da horon daga cibiyar aikin goda ta Jami’ar Ahmadu Bello Zariya wato ( I A R ).

Farfesa Mani shi da abokiyar aikinsa Dakta Luka sun gudanar da mukala masu inganci akan harkar noman zamani da yarda ake yinsa a zamanance

Masanan sun ammasa tambayoyin manoma yayin da suka kammala bayanansu ga mahalatta taron.

Masanan sun bayar da shawara akan yadda ake shuka da yadda ake girbi da yadda ake adana amfanin gona bayan kammala girbi yayin da ruwa ya dauke.

Abdullahi Magaji shine sakataren tafiyar a jawabinsa ya fadi makasudin bayar da tallafin ga manoman.

Magaji yace shugaban gidauniyar ta (SADAKA JARIYA) Honorabul Dauda Iliya ya bayar da tallafin ne don cigaban rayuwar jama’ar karamar hukumar Kudan da jihar Kaduna baki daya.

Kuma yace da ikon Allah manoman karamar hukumar ta kudan zasu zama zakaran gwajin dafi a kasa baki daya da ikon Allah.
Karshe honorabul Magaji yayi kira ga mahalatta taron da suyi amfani da ilimin da suka amfana dashi a cikin fadin karamar hukumar ta kudan da kasa baki daya.

Shiko Sarkin Doka Alhaji Mu’azu Shehu Doka jinjina yayi ga shugaban gidauniyar bisa ci gaban da ya kawowa karamar hukumar ta kudan a bangarori daban daban don haka yayi fatan Allah ya biya masa bukatunsa duniya da lahira.

Malam Muhammad daga shiyar Garu yana daya daga cikin wanda suka amfana da wannan horo da yake zantawa da manema labarai yace sunji dadin horon da suka samu kuma zasuyi amfani da horon ta yadda ya dace.

Bincike ya tabbatar da cewa SADAKA JARIYA FOUNDATION ta bayar da tallafin kiwon lafiya ga mutane masu yawan gaske a fadin karamar hukumar ta kudan a kwanan baya.

Haka zalika wan gidauniyar ta duba bagaren ilmi nanma ta bayar da tallafi ta hanyar biyawa yara kudin zana jaraba ba tare da nuna wani kabilanci ko wariyaba.

Kuma gashi a wannan lokacin gidauniyar ta bayar da tallafin ilmin noma da Irin shuka na zamani( Masara) da taki ga mutane 50 don bunkasa noma a fadin karamar hukumar ta kudan da jihar Kaduna baki daya.

Hakan yasa da yawa al’umma ke yiwa shugaban gidauniyar fatan Alheri.

Leave a comment