Mai Nasiha ya.jagoranci yin addu’oi na nemawa sabon gwamnan zamfara nasara a mulkinsa

Alhaji Salman Mai Nasiha a ya yin addu’oi daya shirya.

An gudanarda taron addu’oi na musamman bayan saukar karatun Qur’ni da akayi domin nemawa zababben sabon Gwamnan jihar Zamfara Alhaji Lawan Dauda Dare taimakon Allah a rantsar dashi ya gudanar da mulkinsa cikin adalci da nasara.

Taron addu’ar da Alhaji Salmanu Mai Nasiha dan jam’iyyar PDP kuma masoyi ga tafiyar siyasar gwamna dare ya shirya aka gudanar a jihar Kano ya sami halartar alarammomi daga sassa daban-daban.

Mai Nasiha, da ma tun fitowar Alhaji Lawan Dauda Dare neman takarar gwamnan Zamfara, yake goya masa baya har zuwa lokacinda aka kai shi qara akan takararsa ma ya shirya makamantar addu’oi irin wannan na neman Allah ya baiwa Gwamnan nasara.

Alhaji Salmanu ya ce wannan saukar Qur’ani da ya jagoranci akayi na godewa Ubangiji ne bisa nasarar da Lawan dare ya samu na zama Gwamnan Zamfara.Da rokon Allah ya yi riko da hannunsa ya kawar da dukkan, matsaloli ya sami aiwatar da ayyuka na kyautatawa jin dadin al’umma.
Bayan saukar an yanka dabbobi da shanu da raguna da raba abinci da hadaya ce ta neman amincewar Ubangiji.

Leave a comment