Kungiyar ‘Yan Jaridun Arewa Sun Karrama Ogan Boye

Bisa irin gudummawar da yake bawa Matasan jihar Kano, da kokarin tabbatar da samar da zaman wato lafiya, kungiyar ‘yan Jaridun Arewa Northern Tourism Journalist’s ” sun karrama Alhaji Yusuf Imam wanda akewa lakabi da Ogan Boye, da lambar Yabo ta girmamawa.

Kungiyar ta kuma bayyana gamsuwarta dangane da yadda Alhaji Yusuf Ogan Boye yake tallafawa ci gaban rayuwar Matasan jihar Kano, ta bangarori daban-daban.

Da yake Mika Lambar Yabon Mataimakin Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Muhammad Auwal Muhammad, yace babu shakka Alhaji Yusuf Imam, ya taka rawar gani wajen ciyar da jihar kano gaba duk da cewa Ogan Boye Dan kasuwa ne wanda ya jajirce domin tabbatar da cewa rayuwar matasar jihar kano ta inganta.

Alhaji Yusuf Imam wanda yana daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda kuma matashin Dan kasuwa ne, kungiyar ta bukace shi da ya ci gaba da irin ayyukan alherin da yakewa matasa wanda hakan yana daga cikin matakan bunkasar ci gaban kasar nan baki daya.

Alhaji Yusuf Imam wanda akafi Sani Da Ogan Boye, ya godewa kungiyar ‘yan Jaridun da suka zakulo shi domin bashi lambar Yabo, inda yayi alkawarin ci gaba da gudanar da abubuwan da ya sanya a gaba domin ciyar da jihar kano gaba.

Leave a comment