Kisan Abubakar Fulatan Da Sa Hannun Shugaban Karamar Hukumar Rogo- ‘Yan Uwan Marigayin

“Muna da tabbacin cewa kisan da aka yiwa Dan mu Abubakar Suleman Fulatan a ranar zaben Gwamna akwa sa hannun shugaban karamar hukumar Rogo saboda yaransa ne sukayi kisan” inji wani daga cikin ‘yan uwan marigayin

A wata ziyara da wakilinmu ya kai a garin Fulatan dake cikin karamar Rogo a jihar, Wanda kuma ya halarci sallar zana’iza. Marigayin, ya tarar da ‘yan uwa da abokan arzikin mamacin cikin jimami na rashin mamacin.

Sun bayyana cewa suna zargin shugaban karamar hukumar ta Rogo da hannu dumu- dumu wajen kisan Dan nasu a cewar su, an daban jam’iyyar APC ne suka kashe Abubakar yayin da ya bayyana cewa shi jam’iyyar PDP zai zaba, inda suka ce kowa ganau ne lokacin da ‘yan daban suka shigo garin Fulatan kuma sukayi abin da suka ga dama na dukan jama’a da Sarar su da muyagun makamai.

” Duk ‘yan daban kowa ya sansu yaran ciyaman kuma sune suka kashe mana Dan mu saboda munyi Allawadai kuma mun barsu da Allah”

Wakilinmu, yayi kokarin jin ta bakin shugaban karamar hukumar ta Rogo, ya shaidawa wakilinmu cewa ” Yanzu ina ofishin ‘yan sanda na Bampai amma idan na gama zan kiraka mu hadu a bakin asibitin Malam Aminu Kano domin yadda lamarin ya yake”

Har ya zuwa lokacin da muke kammala rubuta wannan rahoton, wakilinmu ya kara Neman shugaban karamar hukumar amma baya daukar wayar kuma ya rubuta masa sakon Tes na waya babu amsa.

Har yanzu dai karamar hukumar ta Rogo tana cikin dokar hana zirga-zirga har sai lokacin da zaman lafiya ya dawo.

Leave a comment