ZABEN KANO:  Jami’an INEC Sun Arce Da Sakamakon Zaben Gama

A dai dai lokacin da ake jiran sakamakon zaben mazabar Gama da Yelwa, An yi zargin cewa wasu jami’an kula da akwatin zabe na INEC (Presiding Officer) guda hudu da suka yi aiki a mazabar Gama, karamar hukumar Nassarawa, sun arce da sakamakon wasu rumfunan zabensu da suka harhada.

Kamar Yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. Rahoton ya bayyana cewa kwamishinan zaben jihar Kano, Farfesa Riskuwa Shehu, ya shiga taron tattanawa ta gaggawa da wasu manyan jami’an hukumar domin shawo kan matsalar.

Leave a comment