Bala Muhammad Ya Lashe Zaben Gwamnan Bauchi

Jam’iyyar PDP ta lashe zaben kujerar Gwamna a jihar Bauchi, inda dan takararta Bala Muhammad ya doke Gwamna mai ci Muhammad Abubakar na jam’iyyar APC.

Hukumar INEC ta bayyana sakamakon ne bayan fuskantar tsaiko na kimanin sa’o’i 17.

Bala Muhammad na PDP ya samu nasarar lashen zaben ne da tazarar kuri’u dubu 43,673, bayan samun kuri’u dubu 544,699, yayinda Muhammad Abubakar na APC ya samu kuri’u dubu 588,372.

Bauchi na daga cikin jihohin da hukumar INEC ta bayyana zabukansu na Gwamna da ya gudana a ranar 9 ga watan Maris bai kammala ba, inda a jiya Asabar 23 ga watan na Maris aka karasa zaben a rumfuna 36 da ke mazabu 29 a kananan hukumomin jihar 15.

Leave a comment