An Yi Zaben  Kano Lafiya,  Mutum 10 Kacal Muka Kama Da Aikata Laifukan Zabe– DIG Micheal

Mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya, Micheal Anthony Obizi, ya bayyana zaben Kano da ake kammalawa a matsayin zaben da aka gabatar cikin zaman lafiya.

Obizi, wanda aka turo daga Abuja domin zaben da za a kammala ya bayyana cewa an samu dan hargitsi mara yawa.

Ya kara da fadin cewa rahotannin da ake yadawa a kafofin sada zumunta, wasu mutane daban ne ke kirkira domin su haifar da tashin hankali a jihar.

DIG ya bayyana cewa babu wani rahoton salwantar rai a gaba dayan kananan hukumomi 24 din da aka sake zaben, sannan kuma mutum goma kacal suka kama da aikata laifin zabe.

Ya bayar da tabbacin cewa ‘yan sanda za su tsaya tsayin daka gurin ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Leave a comment