Daraktan Jaridar Leadership Ayau Idris Bala Sulaiman Ya Angwance

Jiya Asabar 23 ga watan Maris, 2019 ne tarihin rayuwar Malam Idris Bala Sulaiman ya sauya, domin kuwa ya sake shiga wata sabuwar rayuwa ta samun karuwar aure da amaryarsa Kareema. Dandazon daruruwan ‘yan uwa, abokai, abokan aiki da makusanta jama’an Annabi ne suka a hallara a birnin Shehu wato Sokoto domin halarta hadi da shaida wannan daurin auren gogaggen dan jaridan.

Idris Bala Sulaiman dai shine sabon babban Darakta da ke kula da jaridar Leadership Ayau a shafin yanar gizo-gizo, gabanin nan, shine Editan jaridar Leadership Ayau, jaridar Hausa da ke fita kullum a Nijeriya.

Idris,Ya aure Malama Kareemah Shehu Ahmad ne bayan da ya cike dukkanin sharudan da addinin Islama ya shimfida.

Leave a comment