ZABEN SOKOTO: Tambuwal Ya Lashe Zabe Da Kuru’u 512,002

An bayyana gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal na jami’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka kammala.

Tambuwal ya lashe zaben ne da kyar da jibin goshi, inda ya sami kuri’u 512,002, yayin da abokin karawarsa na jam’iyyar APC Ahmad Aliyu ya zo na biyu da kuri’u 511,661.

Gwamna Tambuwal ya zarta abokin hamayyar tasa ne da kuri’u 341.

Leave a comment