Zaben Kano Yana Tattare Da Murdiya Da Cin Zarafin Jama’a – Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa zaben gwamnan jihar kano yana tattare ne da murdiya da cin zarafin masu kada kuri’a Inda yace ba zabe bane akayi.

Kwankwanso ya bayyana haka ne a jiya a shafinsa na facebook, yana mai cewa ba a yin zabe a jihar Kano gaba daya sai murdiya kawai ake yi yanzu haka.

Sannan ya yi sharing link yake cewa Mataimakin babban Sufeta Janar na ‘yan sandan Nijeriya DIG Anthony Ogbizi Michael da aka turo Kano ya zo ya karbi ragamar umarni da tabbatar da tsaro ya wargaza dukkan tsarin da aka yi na tabbatar da tsaro.

A wani taron manema labarai da Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Kano Rabiu Sulaiman Bici, yayi a jiya, ya bayyana ya nemi a soke zaben da ake kan gudanarwa a Kano saboda rashi tsaftarsa.

Bichi ya bayyana bukatar hakan ne yayin zantawa da manema labarai a yau din nan, inda yace abinda ke gudana ba zabe ba ne illa shiririta.

Leave a comment