Kungiyar daliban ta karrama Muhammad Sameer Rufa’i Hanga da jakadan zaman lafiya

Daga Ahmad Suleiman Ramat, Kano

Kungiyar dalibai t”National Association of Nigerian students(NANs)”ta bada lambar yabo na jakadan zaman lafiya ga Hon.Muhammad Sameer Rufa’i Hanga.Bisa irin dawainiya da yake na cigaban matasa.
Shugaban kungiyar ta “NANS” kwamared Zahraddeen Yahaya ya ce sun dade suna bibiyar yadda Ambasada Hon.Muhamnad Sameer yake xawainiya da matasa wanda akasarinsu dalibai ne.
Kungiyar .daliban tace , Wannan ce tasa uwar kungiyar ta kasa ta ga cancantar su bashi lambar. yabo ta ambassador zaman lafiya.
Comrade Zahraddeen Yahya
ya kara da cewa Hon Muhammad Sameer Rufa’i Wanda shine shugaban “Wemove” Kwankwasiyya matashine mai son zaman lafiya da kyautata cigaban matasa da ya dace da zama jakadan zaman lafiya.

Shima a nasa bangaren Hon.Muhammad Sameer Rufa’i Hanga ya godewa Allah bisa wannan kyakkyawar shaida da daliban sukayi masa tareda Jan hankalin matasa a koyaushe su zama masu halayya nagari da zasu amfani al’umma.

Hon.Muhammad Sameer ya ce wannan lambar yabo na jakadanci da suka bashi yasa Allah ya cigaba dayi masa jagoranci wajen cigaba da kyautawa cigaban matasa da al’umma gaba daya.

Leave a comment