Kwanaki 100 Na Gwamna Injiniya  Abba Kabir Yusuf Abin Alfahari  Ne Ga Kanawa- inji  Dakta Wailare

Daga Ahmad Suleiman Ramat

An bayyana cikar kwanaki 100 na Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf akan karagar mulki da cewa al’ummar Kano sun shaidi cewa Gwamnati ce tausayin talakawa da son cigabansu.
daya daga cikin masoya kuma magoya baya ga Gwamnan.Injiniya Dakta Saleh Wailare ne ya bayyana hakan.

Ya ce zuwan Gwamnatinsa ta dauki harkar ilimi da muhimmanci wajen gyara matsalolin ilimi da makarantu.Wanda a shekaru Takwas da suka wuce kafin zuwan Gwamnatin Abba an soke tallafinda ake baiwa ya’yan al’umma na biya musu kudin jarabawa a matakin makarantun sakandire.Amma zuwan Gwamnatin NNPP ta dawo dashi ta biyawa yara 55,000 kudin jarabawar NECO.Wannan cigaba ne babba saboda idan jarabawar ta fito yara suna samun damar aiki wasu su cigaba da karatu.

Ya ce ga kuma shiri na tura ya’yan talakawa waje suje su karo ilimi su dawo su bada gudumnuwa ga cigaban al’ummar Kano da kasa baki daya da kuma yin amfani da damar wajen samun aiki a kasashen duniya da zasu taimaki Kansu da yan’uwa da iyaye da al’ummarsu.

Dakta Saleh Musa Wailare
ya yi nuni da cewa a wajensa vangaren ilimi da aka kalla ko da shi kadai ne wannan Gwamnati ta dauka ya isa ace Gwamnati ce da tasan yakamata mai son cigaba da son ganin cigaba da yawa.

Ya ce duk shugabanci da ya kulada ilimi shine abin alfahari da za’a sami cigaba a cikinta.Dan haka suna godewa Allah bisa yanda Gwamnati ta baiwa ilimi muhimmanci ake maida ya’yan talakawa su zama masu ilimi da za’ayi alfahari dasu a Kano da kasa da kasashen Duniya saboda da ilimi ne mutum zai san damar sa da yancinsa ya yi gogayya da wasu yama san abinda zai tashi ya faxi abinda zai kawo cigaban al’ummar sa.

Dakta Saleh Musa Wailare yace mu anan mungodewa Allah bisa irin wannan kokari da hangen nesa na Gwamnan akan bunqasa ilimi.
Ya kara da cewa ba wannan kawai ba irin matakai da Gwamnan Abba Kabir ya dauka na ragewa al’ummar Kano halin kuncin rayuwa abune mai kyau domin an rabawa dinbin mabukata kayan abinci da tallafawa manoma da kayan noma ga kuma ayyuka daban -daban da ake na kwashe shara da dawo da fitilun tituna da kuma yashe magudanan ruwa da inganta harkokin lafiya ta kulada gyara Asibitoci.

Dakta Saleh Musa Wailare ya ce zuwan Gwanna Abba ya dawo da Asibitin yara na Hasiya Bayero da a baya akaso a salwantar yanzu an gyara ana aikin kulada lafiyar yara.
Dakta Saleh Musa Wailare ya ce da yardar Allah wannan Gwamnati zata cigaba da ayyuka na cigaban al’umma cikin nasara ta gama wa’adinta na farko ta rora a karo na biyu.

Leave a comment