Masarautar Machina Itace Kan Gaba Wajen Iya Hawan Daba Da Wasan Kokawa A Nijeriya                     … Inji Sarki Bashir 


Mai Martaba Sarkin machina a jihar Yobe, Alhaji Bashir Albashir  Bukar machinama, ya bayyana cewa masarautarsa itace kan gaba wajen iya hawan daba a fadin Nijeriya.
Sarkin ya bayyana cewa run sama da shekaru 1000 masarautarsa take zama kan gaba wajen hawan daba a nahiyar Afrika Wanda hakan ya sanya har yanzu suke riko da al’adusu.


Ya bayyana haka ne a jawabinsa yayin rufe bikin al’adun masarautar na wannan shekarar a garin machina dake jihar yobe.

​An gudanar da gasar wasannin gargajiya na kokawa da Gudun langa wato wasan gudu da kafa daya. Sai kuma wasan hawan daba Wanda shine wasa mafi kayatarwa a bikin.

Gundumomi biyar ne na masarautar machina suka fafata a cikin wasan wanda gundumar machina da Falmaran suka samu zuwa mataki na karshe a cikin duk wasannin da aka gudanar.

Gundumar  machina itace tazo ta farko a wasan langa sai  Falmaran  tazo ta biyu.

A wasan kokawa kuma gundumar Machina itace  Tazo ta farko sai gundumar Falmaran  tazo ta biyu.

Dan kokawa Babani Malam Sani  daga Gundumar Machina shine ya lashe gasar A matsayin sarkin kokuwa na machina na shekarar 2017. Babani shine Wanda ya fara lashe gasar kokuwa na farko a masarautar machina a shekarar 2016 wanda kuma yanzu bayan an kwashe shakaru biyar ba’a gudanar da wasan ba sai wannan shekarar wanda kuma shi babani ya kara ajiye tarihi na lashe gasar 


Masarautar machina wacce ta kwashe sama da shekaru 1000 da samuwarta, ta kunshi kabilun Mangawa da Hausawa da Fulani.

An fara gudanar da bikin raya al’adun masarautar ne a shekarar 2003 biyo bayan nasarar da ta samu a bikin raya al’adu na Nijeriya a shekarar 2002.

Taron wanda shine karo na biyar, ya samu halarcin sarakunan gargajiya daga jihohin Nasarawa da jigawa da kasar Nijar. Sauran manyan bakin da suka halarci taron sun hada; ‘yan majalisun tarayya dana jiha da kwamishinonin da shugabannin kananan hukumomin jihar Yobe da kuma ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa daga ciki da wajen jihar Yobe.

Leave a comment