Akwai Bukatar Gwamnatin Tarayya Ta Samar Da Masana’antar Markada Karafa A Arewa

Masu Sana’ar Karafa na Arewacin Nijeriya sun bukaci gwamnatin tarayya data samar da masana’antar markada karafa  a Arewa wanda hakan zai taimaka wajen habbaka tattalin arzikin yankin da kuma samawa matasa ayyukan yi.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kamfanin hada-hadar karafa na( FABSON SCRAPT VENTURES) Alhaji Abba Aminu, a zantawarsa da manema labarai a Kaduna inda yace akwai bukutar gwamnatin tarayya ta Samar da masana’antar  markada karafa saboda duk karafan da ake kaiwa jihar legas daga Arewa ake samosu, a cewarsa, Arewacin Nijeriya na bukatar masana’antu wanda hakan zai taimaka wajen samawa matasa ayyukan yi.

Alhaji Abba, wanda akafi sani  da (GWASKA IKON ALLAH) yace, sana’ar karafa tana taimakawa wajen samawa matasa ayyukanyi yana mai cewa, a kamfaninsa kawai akwai matasa sama da talatin da suka amfana da kamfanin Wanda wasunsu yanzu duk sun bude nasu kamfanonin

Akan hakan, Shugaban ya bukaci matasa da su tabbatar da cewa sun kama sana’a domin dogaro da kansu.

Leave a comment