Samar  Da Zaman Lafiya Shi Na Sanya A Gaba  …Inji Ibrahim Sambo

Kungiyar Matasan kasashen Afrika (African Youth Assembly For Peace)  AYAP ta karrama Alhaji Ibrahim Sambo Magnet da lambar yabo na jakadar zaman Lafiya na Afrika bisa irin gudummawar da yake bayarwa na tabbatar da zaman Lafiya  a kasashen Afrika da kuma tallafawa matasa da yakeyi a fannoni daban daban.

Kungiyar ta kuma bayyana Ambasada Ibrahim Sambo , da cewa a duk fadin Afrika babu wani mutum da yake bayar da lokacinsa sa dukiyar domin Samar  da zaman Lafiya musamman a tsakanin matasa kamar Ibrahim Sambo Wanda a cewarsu ya kawo ci gaba a rayuwar matasan Afrika baki daya.

An gudanar da taron karramawar ne a dakin taro na gidan Sardauna dake jihar Kaduna a ranar lahadin karashen mako, taron da ya samu halarcin manyan mutane daga kasashe daban daban na Afrika da kuma nan kasa Nijeriya.

Da yake jawabi, a wurin taron Ambasada Ibrahim Sambo, ya bayyana cewa Samar da zaman Lafiya da tallafawa matasa maza sa mata  sune abubuwan  da ya Sanya a gaba Wanda kuma zai ci gaba da gudanar da su.

A hakan ya bukaci daukacin matasa da su tabbatar sun Kawo abubuwan da zasu taimaka wajen Samar da zaman Lafiya a fadin kasar nan dama Afrika baki daya Wanda shine ginshikin ci gaba.

Leave a comment