Aikin Gwamnati Na Matasa Ne Saboda Ni Na Tsufa Da Zama Gwamna … Inji El-Rufa’i

 

Gwamnan  Jihar Kaduna, Nasir  Ahmed El-Rufai, ya bayyana kansa a matsayin mutumin da ya tsufa da zama Gwamna.

Da yake magana a Kaduna kan bukatar sake fasalin ma’aikatar jihar, El-Rufai ya mayar da hankali kan cewa akwai bukatar matasa da ‘yan Najeriya masu gwaninta su shugabanci jihohi a kasar.

Gwamnan ya nace kan cewa ba wa matasa damar shugabantar kasar shi ne hanya mafi dacewa.

“Aikin gwamnati na matasa ne, na yi tsufa da zama Gwamna. Ya kamata a ce na zamo Gwamna lokacin da nake shekaru 40.

“Wannan shekarun ne ya kamata saboda lokacin mutum na da kuzari, mutum na da gwanancewa, mutun na iya daukar dogon sa’o’i. Na san yawan sa’o’in da nake dauka lokacin da nake a matsayin ministan Birnin tarayya, ba zan iya yi haka ba a yanzu.

“Ya kamata mu ba matasa hanya sannan kuma a Kaduna, muna aiki a kan haka.”

Tsohon Ministan Babban Birnin tarayyar, ya bayyana cewa gwamnatinsa na duba ga sake faslin al’amuran gwamnatin jihar don inganta jihar.

Leave a comment