‘Yar Nijeriya Ta Zo Ta Biyu A Gasar Rubutu Na Duniya

Daliba ‘Yar Nijeriya, Misis Ngozi Razak Soyebi da ke Kwalejin Zamani (Zamani College) da ke Kaduna ta zo ta biyu a gasar rubutu ajin malamai da aka kira (Commonwealth Class Story Writing Competition for Teachers) a Turance inda ta sami nasara a kan marubuta fiye da kasashe 52 na kungiyoyin kasashe renon Ingila da suka shiga gasar a dukan fadin duniya.

A wannan gasar rubutun wadda ta zo na daya wata Malama ce daga kasar Indiya mai suna Nandini Dasgupta wadda kididdigar alkaluman makinta ya dara na Misis Ngozi Razak Soyebi da ta zo na biyu, sannan kuma wadda ta zo na uku, ‘yar kasar Ingila ce mai suna Caroline Picking.

Rahotanni sun nuna cewa, malamai ‘yan Najeriya sun shiga gasar nan kuma sun yi iyakacin bakin kokarinsu inda suka sami nasarar samun matsayi a cikin 10 na farko a cikin su fiye da mutum dubu uku da suka shiga gasar daga dalibai da malamai na kasashe renon Ingila. Taken gasar na bana dai shi ne. ‘’Belonging’’.

Malaman da suka sami shiga matsayin nan na goman farko ‘yan Najeriya su ne, Misis Olamide Aluko daga makarantar American Christain Academy da ta zo na 6, a labarinta mai taken ‘’ Mojisola’’. Sai wani malami Peter Brown daga Kwalejin Thomas Adewumi da ke Jihar Kwara da ya zo na 8 a labarinsa mai taken ‘’Belonging’’, sannan kuma akwai wata malama daga Sakandaren Gwamnati da ke Kubwa, Abuja mai suna Misis Vera Obiakor da ta zo na 9 ita ma a labarinta mai taken ‘’Belonging’’.

Wannan gasar dai hadin gwiwa ne da ofishin Jakadancin Burtaniya da Sakatariyar kungiyar kasashe renon Ingila domin su dinga hada makarantu da matasan mutane masu baiwar rubutu na yankunan duniya a tsarin koyarwar hadin gwiwa.

Labarin ita Malama Ngozi Razak Soyebi ‘yar Najeriya da ta zo na biyu ya dubi batu ne na gwagwarmayar wani yasashshe yaro (Ibrahim) a kan titi na Najeriya. Ta yi wa labarin nata taken ‘’Kodayaushe Akwai Lokaci Na Farko’’, wato ‘’There’s Always a First Time’’ a Turance.

A nata jawabin a wurin taron da aka yi domin bai wa wadanda suka sami nasara satifiket a gasar a Abuja, Daraktar Tsare-tsare ta ofihin Jakadancin Burtaniya, Misis Louisa Waddington ta ce, ofishinsu na tallafa wa makarantun da suka nuna suna son shiga tsarin azuzuwa na kungiyar ta Commonwealth don yin gasa, muhawara da musu a fadin duniya da gasar rubuce-rubuce na malamai da dalibai.

Ta ce, tantance ka’idojin shiga gasar ya sami dubawar tsohon mai rike da kambun adabi da wasu kyaututtuka, matashi Anne Fine da kuma wata tsangayar ‘Arts’ a ofishin Jakadancin Burtaniya, kuma ta ce duk shigar da ofishin nasu ya yi a gasannin da suka gabata a baya na ajin Commonwealth, ya tallafa wa malamai da dalibai da suka sami nasarori inda suka kai su suka kalli gasar wasannin Glasgow, wato ‘’Glasgow Commonwealth Games’’.

Leave a comment