Ricikin APC: Gwamnatin Kaduna Ta Rushe Gidan Matamakin Shugaban  APC Na Kasa


A yau ne gwamnatin jihar Kaduna ta rusa gidan mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa Inuwa Abdulkadir da ke kaduna.
Gidan wanda yake akan titin Yakubu Avenue, hukumar kula da tsara birane na jihar KASUBDA sune suka rusa gidan.

Dama dangantaka tsakanin gwamnan Nasiru El-Rufa’i  da shugaban jam’iyyar inuwa Abdulkadir tayi tsami sakamakon rikicin gida na jam’iyyar tsakanin bangaran gwamna  da  sanata shehu sani.


Cikakkan rahoton rusa gidan zai biyo baya nan gaba.

Leave a comment