Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ya tallafa wa daliban BUK 628

Daga Shehu Usman Yahaya

 Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya tallafa wa dalibai 628 na Jami’ar BUK.

An zabo daliban ne daga mazabar Kano ta Arewa, inda yake wakilta, inda aka ba kowane dalibi Naira N50,000.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon tallafin a ranar Litinin, Shugaban Ma’aikatan Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, Farfesa Muhammad Ibn Abdullahi ya ce Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya yanke shawarar tallafa wa daliban ne domin taimaka masu su samu damar cigaba da karatunsu.

A wata sanarwa da mai ba Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan shawara na musammana a kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir ya fitar, ya ce za a fadada shirin zuwa dukkan sauran daliban yankin Kano ta Arewa da suke karatu a sauran manyan makarantun da suke kasar nan. 

“An shirya bayar da tallafin nan ne ga daliban da suke karatun digiri na farko daga yankin Kano ta Arewa. Kowane dalibi zai samu Naira 50,000 daga Sanata Barau I’ Jibrin.

“Wannan tallafi ba ga daliban BUK kawai zai tsaya ba, duk wani daliban Kano ta Arewa da ke karatu a Najeriya zai amfana da wannan shirin. Ba wannan ba ne karo na farko, domin Sanata Barau I. Jibrin ya dade yana bayar da irin wannan tallafi musamman ga manoma da sauransu,” inji shi.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci moriyar tallafin da su dage wajen karatunsu domin samun sakamako mai kyau.

Daya daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin, Adama Iliyasu Rabi’u, wadda daliba ce da ke aji hudu ta yi godiya ga Sanata Barau I. Jibrin  bisa wannan tallafi da ya ba su.

“Muna godiya da wannan tallafi da aka mana. Yanzu zan je in karasa rajista dina. Ina matukar godiya ga Sanata Barau I. Jibrin, Allah Ya saka masa da alheri.” Inji ta.

Shi ma Shamsuddeen Usman cewa ya yi, “Na karbi tallafin Naira 50,000. Ni dalibi ne da ke aji uku, kuma dama ina cikin wani yanayi na biyan kudin makaranta. Ina godiya ga Sanata Barau I. Jibrin.” 

Leave a comment