Kungiyar NUTRW Zata Tallawa Direbobi 300  A kaduna

Daga Shehu Yahaya 

Shugaban kungiyar direbobi ta qasa NURTW reshen Jihar Kaduna ,  Alhaji Aliyu Tanimu Zaria, ya  bayyana cewa a  kalla direbobi 300 ne zasu amfani da tallafin kungiyar domin rage musu radadin kuncin rayuwa da ake ciki biyo Bayan cire tallafin man fetur da gwamnati tayi.

Shugaban yace ganin irin halin da cire tallafin man fetur ya Jefe al’umma a ciki, Hakan ya Sanya kungiyar su ta yanke shawarar tallafawa direbobi da tallafin kudi domin rage musu radadin Kuncin rayuwa. 

Alhaji Aliyu Tanimu Zaria, wanda kuma shine Zabebben  mataimakin Shugaban kungiyar ta kasa Mai wakiltar Arewa,  ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a ofishin kungiyar dake Kaduna, Yana Mai cewa zasu  zakulo direbobi ne daga kananan hukumomin jihar 23.

Ya ci gaba cewa ” Ganin halin da direbobi suke ciki bisa cire tallafin man fetur, shi yasa  muka ga ya dace mu basu tallafin kudi, Idan kuka duba yanzu Zaku ga cewa direban da ka zuwa Zariya sau biyu ya koma sau xaya wanda kuma yake zuwa sau daya yanzu Sai yayi kwana biyu Baiyi lodi ba Yana Zaman dirshen  a tasha kuma ga iyalai yana da su kuma  ga tsadar man fetur;  babu fasinja, shi yasa muka yanke shawarar basu tallafin kudi domin rage musu radadin rayuwa”

“Muna Da shiyyoyi daban-daban a tashoshin mu a daukacin kananan hukumomin jihar Kaduna, wanda ta nan ne  zamu bi mu dauko su daga ciki. Ko babu komai dai idan kaba direba abinda zai ci a gidansa na kwana daya ai kunga an dan rage wani abu” 

” Muna godiya da abinda gwamnan jihar kaduna Uba Sani yayi mana, na Sanya kungiyar mu cikin wadanda zasu amfani da tallafin cire man fetur da gwamnati zata rabawa al’ummar jihar kaduna, duk da cewa yace mu xan Dakata saura kaxan layin zaizo kanmu, muna godiya sosai” inji shi.

Alhaji Aliyu Tanimu Zaria, ya bukaci daukacin ‘ya’yan kungiyar da suke Arewacin Nijeriya da su ci gaba da basu goyon bayan da ya kamata, a cewarsa,  a matsayinsu na shugagannin kungiyar zasu yi iya bakin  kokarin wajen ganin wajen hada kan ‘ya’yan kungiyar Baku daya.

Shugaban yace burinsu shine su inganta rayuwar direbobi a Arewacin Nijeriya dama kasa baki daya.

Akan Hakan ya shawarci waxanda suka yi takara a kujeru daban-daban a kungiyar basu samu nasara ba da su zo su haxa hannu wuri daya domin ciyar da kungiyar gaba a matakai daban-daban a fadin kasar nan baki daya

Leave a comment