Kungiyar Mawallafa Jaridu Da Mujallu  Ta Jihar Kaduna Ta Karrama Shugaban Kamfanin Gallma Multipurpose 

Alhaji Umar Abubakar Rike Da Lambar Yabon Da Aka Bashi

Kungiyar  Mawallafa Jaridu da Mujallu ta jihar Kaduna ta karrama shugaban kamfanin   Gallma Multipurpose Nigeria Limited  Alhaji Umar Abubakar da lambar yabo bisa irin gudummawar da yake bayarwa wajen tallafawa rayuwar matasa da ci gaban kasa.

 Kungiyar ta bashi lambar yabon ne a yayin taron shekara-shekara ma Kungiyar wanda aka gudanar dashi a dakin taro na Gidan Sardauna dake Kaduna.

Daga Dama: Alhaji Umar Abubakar, Jafaru Maitama Ihima Sai Sakataren Kamfanin Gallma Multipurpose Nigeria Limited

 Shugaban kungiyar  Jafaru Maitama Ihima ya bayyana  cewa sun zabi Alhaji Umar Abubakar ne domin nuna kishinsa da kuma bayar da gudunmawar wajen  sadaukar da kai da ayyukan jin kai a jihar Kaduna da kasa baki daya.

 Da yake ba da lambar yabo, shugaban kungiyar na kasa Jafaru Maitama Ihima, ya ce an ba shi lambar yabon ne a bisa kokarin da yake yi na karfafa matasa da samar da ayyukan yi wanda hakan ya zama abin yabawa ga kafafen yada labarai na jihar Kaduna. 

Da yake karbar lambar yabo, Darakta Kamfanin  Gallma Multipurpose Nigeria Limited, Alhaji Umar Abubakar, ya yaba da wannan lambar yabon, inda ya yi alkawarin bayar da mafi kyawun sa a koyaushe.

 Daraktan ya bayyana cewa zaben da aka yi na ba shi lambar yabo ya cika, kuma yadda aka ba shi lambar yabo ya sanya shi a zuciya.

Alhaji Umar Abubakar, Ya nuna matukar jin dadinsa da karramawar da aka yi masa, ya kuma yi nuni da cewa wannan karramawar zata  kara masa  himma da yin hidimar al’umma da kawo ci gaban kasa baki daya.

Leave a comment