Gwamnatin Kaduna Tayi Kyakkyawan  Tanadi Ga Manoma A Kasafin 2024-  Inji Honorabul Bello

Daga Shehu Yahaya

Shugaban Kwamitin Kula da Harkokin Noma a Majalisar Dokokin jihar Kaduna Honorabul Abdullahi Muhammad Bello, ya ce manoma a fadin Jihar za su dara sakamakon kyakkyawan tanadi da gwamna Uba Sani ya yi musu a cikin kasafin kudin shekarar 2024.

Honorabul Abdullahi Muhammad Bello ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin ganawarsa da wakilanmu.

Honorabul Abdullahi Muhammad Bello wanda ke wakiltar mazavar Maigana dake yankin karamar Hukumar Soba yace a cikin kasafin kudin bana Gwamna Uba Sani ya ware wa harkar noma tsabar kudi  naira biliyan 17 wanda za’a yi amfani dasu wajen gina hanyoyi da za su taimakawa manoma dake karkara domin saukaka musu wajen fitar da amfanin gonar su.

“Gwamnatin jihar Kaduna karkashin kwamitin da nake jagoranta a majalisa da hadin gwiwar ma’aikatar harkokin noma na aiwatar da wani shiri da zai taimakawa Manoma a fadin jihar wajen saukaka musu hanyoyin gudanar da harkokin noma ta hanyar wadata su da ingantaccen taki da samu tallafin daga gwamnatin tarayya domin cikar muradi”

Dan Majalisar ya kuma sha alwashin yin dukkanin mai yiwuwa a karkashin kwamitin da yake jagoranta wajen ganin manoma a fadin Jihar sun samu tagomashin da ya kamata kasancewar shi manomi  ne wanda ya jima a cikin harkar.

Honorabul Abdullahi Muhammad Bello ya kuma yi kira ga Matasa a faxin Jihar musamman wadanda suka kammala karatu suna zaman jiran samun aikin gwamnati, da cewar su rungumi sana’ar noma domin ita ce za ta yanke talauci kuma tushe ne na arziki ga dukkanin mai bukata.

Leave a comment