Gwamnatin Buhari Itace Mafi Muni A Tarihin Duniya – Mahdi Shehu


Dakta Mahadi Shehu

Daga Shehu Yahaya

Fitaccen Dan gwagwarmayar mai fafutukar yaki da cin-hanci da rashawa, Dakta Mahadi Shehu, ya bayyana cewa gwamnatin tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari itace silar jefa al’ummar kasar nan halin da suke ciki na kuncin rayuwa da taɓa arzikin kasar.

Mahadi Shehu, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai a Kaduna inda ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta gayaci tsohon shugaban kasa domin bayar da ba’asin yadda akayi Wasoso da dukiyar alummar kasar nan.

“Tun daga zamanin Annabi Adamu har zuwa yau ba a taba wani shugaba wanda shi da mutanensa na kusa da na nesa suka yaudari mutane, suka ci amanar mutane; suka karya kasa suka kashe kasa, suka wulakanta kasa irin Buhari da mukarrabansa ba”

Mahadi Shehu ya ci gaba da cewa “Buhari da makusantansa sune suka kawo tsananin talauci, yunwa da fatara a kasarnan; su suka kawo karayar arziki ta mutane ƴan kasuwa da manoma. Duk wani bala’i da muke ciki Buhari ne sila sanadiyyar rashin sanin makamar mulki”

“A karƙashinsa aka kashe dubban mutane, an kone Dukiya wadda ba ta da iyaka. Buhari ne babban hatsarin da ya faxa wa Nijeriya” inji shi.

Leave a comment