’Yan Banga Ake Zargi Da Kashe Malamin Addini Ba, Askarawan Zamfara Ba – Gwamnati

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara

Aƙalla mutane goma da ake zargin ’yan ƙungiyar ’yan banga ne aka kama bisa zargin kisan wani Malamin addinin Islama a Jihar Zamfara.

Wasu da ake zargin ’yan banga ne suka kashe Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada da ke Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar Talata.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa waɗanda ake zargin da jami’an tsaro suka kama ’yan banga ne ba Jami’an Rundunar Kare Jama’a ‘Askarawan Zamfara’ (CPG) ta jihar ba.

A cewar sanarwar, gwamnatin Zamfara ba ta lamunce wa ’yan bangan da aka kama gudanar da kowane irin aikin tsaro ba, saboda ba sa cikin rundunar kare jama’a ta jihar.

“Gwamnatin Jihar Zamfara ta samu labarin kisan gilla da aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan Mada a garin Mada. Lallai wannan abin takaici ne da za a iya kauce ma shi.

“Jami’an tsaro sun yi nasarar cafke duk ’yan banga da ake zargi da aikata wannan ɗanyen aikin.

“Gwamnatin Jihar Zamfara ta ɗauki wannan lamari da muhimmanci kuma ta himmatu wajen ganin an gurfanar da duk waɗanda suka aikata wannan kisan gilla a gaban kotu. Za a yi duk mai yuwuwa don ganin an yi adalci ba tare da tsangwama ba.

“Muna so mu fayyace cewa ‘yan bangan da ake zargi da aikata kisan gilla ba su da wata alaƙa da Askarawan Zamfara.

“An kafa Rundunar Kare Jama’a a Zamfara ne don kare al’umma, ba wai zaluntar mutane a jihar ba.

“Wannan ƙarin bayani zai kawo ƙarshen ruɗanin da ya taso game da haƙiƙanin alamin wanda aka kama da hannu a wannan kisan gilla. Ba za mu taɓa gazawa ba, wajen kare rayuka da dukiyar jama’a.

“Muna so mu sanar da jama’a cewa jami’an mu na hukumar kare jama’a (Askarawan Zamfara), suna da tsarin gudanar da ayyukan su, wanda ya hana su gudanar da aiki ba tare da jagoranci, ko shiryarwa daga jami’an tsaro ba.

“Binciken farko na ‘yan sanda da ya fara fitowa game da wannan lamarin, ya nuna cewa ɗaya daga cikin ‘yan Bangar da aka kama, ya kasance tsohon ɗalibin Malamin ne. Wannan labari zai taimaka ma Hukumomi sanin haƙiƙanin matsalar, tare da ɗaukar matakan da suka dace.

“Gwamnatin Zamfara za ta sanar da sakamakon binciken ‘yan sanda game da lamarin, da zarar sun kammala binciken su.

“A wannan hali na juyayi, muna miƙa saƙon ta’aziyyar mu ga iyalan Sheikh Abubakar Hassan Mada, ‘yan uwa da al’ummar Mada gaba ɗaya. Allah gafarta masa, ya sa aljanna ce makomar sa.

Leave a comment