Kungiyar GOPRI Ta Kudiri Aniyar Tallafawa Matasa Masu Shaye -shaye A Kaduna 

Dakta Melvin Ejeh

Daga SHEHU YAHAYA

DAGA SHEHU YAHAYA

Wata Kungiya mai rajin yaki da shaye-shaye da Tallafawa rayuwar matasa ( Global Peace and Life Rescue Initiative) GOPRI ta Tallafawa Matasa Masu Shaye -shaye  su 50  Da Kayan tallafin da zasu fara sana’a a jihar Kaduna.

Kungiya tace sun dauko matasan ne daga Kananan hukumomin tsakiyar jihar Kaduna guda bakwai Wanda yanzu aka koya musu sana’ar da zasu dogara da kansu.

Da yake Bayani a wajen Taron da Kungiyar ta gudanar a Kaduna, Babban Daraktan kungiyar Dakta  Melvin Ejeh, yace Taron haxin gwiwa da hedikwatar tsaro ta Nijeriya karkashin jagorancin Janar Christopher Musa, Inda suka kudiri aniyar sauya rayuwar matasa da suke jihar Kaduna.

“Mun shirya Wannan taro ne Domin  wayar da kan Yara matasa  akan illar shaye -shaye  da Kuma lalubo hanyar da zamu tallafa musu Domin su Daina Shaye-Shaye”

Yanzu haka Muna da  matasa Masu shaye shaye guda 50 da muke Kula da su Wanda idan an kammala Wannan Taron zamu basu tallafin da zasu je su fara sana’ar da zasu dogara da kansu. Wannan taro Janar Christopher Musa ne ya kauki nauyin gudanar da shi wanda an gudanar da Irin Wannan taro a kudancin jihar Kaduna, yanzu Kuma mun dauko matasa daga kananan hukumomin bakwai Dake  tsakiyar jihar Kaduna Domin Suma su amfana da wannan Shiri” inji shi.

Akan Hakan , Dakta Melvin Ejeh, ya bukaci matasa da su kaucewa tu’ammali da muyagun kwayoyi Wanda ke da illa ga c gaban rayuwarsu.

Haka Kuma ya yaba da kokarin Hafsan Tsaran Nijeriya Janar Christopher Musa Bisa jajircewasa wajen Tallafawa rayuwar matasa da fasin kasar Nan Inda yace matasan jihar Kaduna sun gamsu da yadda yake Tallafawa rayuwarsu.

A zantawarsu  da wakilinmu wasu matasa Masu Shaye -shayen mayagun kwayoyi da suka halarci wurin Taron sun bayyana gansuwarsa dangane da Taron Inda suka muddin za’a rinka taimakawa rayuwarsu Babu shakka zasu Daina Shaye-Shayen duba da yadda rayuwarsu take cikin hadari.

Taron ya samu halarcin manyan jami’an soja da ‘yan sanda da na Hukumar yaki da Sha da fataucin muyagun qwayoyi da kungiyar Fulani ta Miyeeti Allah da malaman addinai daga kananan hukumomin tsakiyar jihar Kaduna.

Leave a comment