Muna Goyon Bayan Shirin Gwamnatin Tarayya Na Fara Amfani Da Motoci Masu Amfani Da Iskar Gas-  Rugoji


Alhaji Haruna Musa Rugoji



Daga Rabi’u  Haruna Dankani,  Kaduna


Shugaban Hukumar Sufuri Ta jihar Katsina ( KSTA) Alhaji Haruna Musa Rugoji, ya bayyana cewa suna goyon bayan Shirin gwamnatin tarayya na fara yin amfani da Motoci Masu Amfani Da Iskar Gas a fadin kasar Nan.
A zantawarsa da manema labarai a Kaduna  yayin gudanar da  taron masu ruwa da tsaki akan harkar sufuri ,  shugaban hukumar, ya Yaba da tsarin gwamnatin tarayya na samar da Shirin inda yace zai amfani  talakawan kasar Nan Baki Daya

Haruna Musa Rugoji yace  “gwamnatin tarayya Ta fito da wannan tsarinne domin rage wa talakawa radadin cire tallafin mai da akayi musamman akan abun da ya shafi sufuri”

Shugaban  yayi Kira da roko ga gwamnatin tarayya inza kaddamar da wannan Shiri na motoci masu amfani da iskar gas a fara da jihar Katsina musamman in akai duba da irin biyayya da goyon baya da suke bayarwa.

Shugaban hukumar Haruna Musa Rugoji ya kara da cewa jihar Katsina ta shirya tsaf da bin wannan tsari wurin canza motocinsu izuwa amfani da iskan gas domin sauwakewa talakawa kudin zirga zirga.

Rugoji ya kara da cewa a cikin abun dake cima mai girma Gwamnan jihar katsina tuwo a kwarya , bayan tsaro shine sufuri,  shi yasa yana shigowa offis  baifi wata biyu ba ya siyo motoci guda  40  domin rage wahalar zirga- zirga ga alummar jihar katsina.

A karshe Haruna Musa rugoji yayi Kira ga alummar jihar Katsina  Su ci gaba da baiwa mai girma gwamna Dikko Umar Radda goyon baya domin ciyar da jihar gaba.

Leave a comment