Adduo’i  Ya Kamata Muyi Ba La’antar   Shugabanni Ba- Turakin Bai Zazzau

Barista Ibrahim Bello Rigachikun ( Turakin Bai Zazzau)




Daga Rabiu Haruna Dankani,  Kaduna

A yayin da ake ci gaba da gudanar da bukukuwan sallah a Jihar Kaduna, an Buƙaci Al’umma da su ci gaba da yiwa shugabanni addua maimakon la’antarsu.


Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban mai taimakawa Gwamnan jihar Kaduna a bangaren masarautu,  Barista  Ibrahim Bello  Rigachikun,a  zantawarsa da manema labarai.

Bello Wanda Kuma shine  Turakin Bai Zazzau,  yace ba karamin abun farinci bane ace anyi sallah lafiya Angama lafiya.

Basaraken ya bayyana  farin cikinsa wurin jajircewa da adduo’i da alummar wannan kasa sukeyi domin  samun nasara da ciga mai dorewa sa’annan ya yaba wa malamai bisa tunartar  da al’umma ta kafafen sada zumunci Irin adduo’i da ya kamata dukkan musulmi suyi a wannan ranar sallar Layya.

Da yake bayanin akan mahajjatan kasar nan kuwa Turakin Bai Zazzau yace gaskiya alhazan kasar nan sunyi abun azo a gani yayin gudanar da Ibada Akasa mai tsarki musamman wurin bin doka da oda akan sharuddan da hukumar alhazai ta gindayamasu tare dafatan Allah yakarbamasu adduo’in dasukayi yakuma dawomana dasu lafiya.

Ya Kuma   yayi Kira ga al’umma da su daina la’antar  shuwagabanni inda ya e addua ya kama su dunga masu domin ci gaban Nijeriya Baki Daya .

Leave a comment