Gwamnatin Kaduna Ta Dakatar Da Aikin Gina Magudanar Ruwa

nasir-elrufai-2

Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci daukacin ýan kwangilar da suke aikin gina magudanar ruwa a cikin kwaryar jihar da su dakatar da aikin su har sai ta bukace su bisa wasu dalilai wanda bata bayyana su ba.
Gwamnatin jihar a karkashin jagorancin Gwamna Nasiru El-Rufaí, ta fara aikin gina magudanar ruwa a yankuna daban-daban na cikin jihar, aikin wanda da jamaä suke ganin ya fara jawowa gwamnatin farin jini a cikin a fadin jihar, hasalima jamaá suna ta yiwa gwamnatin sam barka da fara aikin.
Wata majiya ta shaidawa wakilinmu cewa gwamnatin ta bayar da umarnin dakatar da aikin ne yau laraba, bisa ga wasu dalilai da bata bayyana su ga jama’ä ba, sai dai majiyar shaida mana cewa wannan umarni yana da nasaba da rashin masu kula da aikin da kuma rashin ingancin aikin da ‘yan kwangilar suke gudanarwa da.

aaaa
Yayin da wakilinmu ya kai wata ziyarar aiki a ofishin hukumar kula da gyaran hanyoyin jihar wanda itace ke gudanar da aikin magudanar ruwan (KAPWA) ya tarar da manyan jami’an hukumar a rude , inda wasu suka tsegunta masa cewa yanzu haka an bukace su da su dauki motoci su bazama duk inda ake gudanar da aikin magudanar ruwa su dakatar da aikin, inda domin dakatar da aikin cikin gaugawa.
Sai wani bincike da muka gudanar ya nuna cewa mafiya yawan kwangilar da ake yi na magudanar ruwan ýan jamíyyar adawa na PDP suke yinta, saboda sune suke sayan kwangilar daga hannun wadanda gwamnati ta ba su kwangilar aikin. Hasalima, sune suke da kudi a hannun na yin aikin musamman ganin cewa gwamnati bata biyan kudi ga dan kwangila sai ya fara aiki kuma sai aikin ya kai ga wani mataki kamin zaá biya shi kudinsa.
A kwanakin baya ma gwamnatin jihar ta cire wani darakta a hukumar bisa zargin shi da cewa ya aikita ba dai-dai ba duk kuwa da cewa darakta shine yake jagorantar aikin wanda kuma jama’ä suna amfana da aikin.
Munyi kokarin jin ta bakin shugaban hukumar ta KAPWA amma hakan yaci tura wanda aka bayyana cewa yana wani zama gwamna. Har lokacin da muke kammala rubuta wannna rahoto babu duriyarsa.

Leave a comment