An Hana Shugaban Hukumar KAPWA Fita Daga Ofis Saboda  Bashin Miliyan 4

A yau ne wasu matasa ‘yan kasuwa masu harkar man Gas a jihar Kaduna suka hana shugaban Hukumar kula da gyaran hanyoyi na jihar Kaduna (KAPWA) Mista Martin, fita daga harabar Hukumar bisa rashin biyansu kudin su da baiyiba.

Matasan wadanda suka shigo Hukumar da misalin karfe 12 na rana, sun rufe kofar da shugaban zai fita da motarsu kirar 406, inda suka dauki alwashin cewa ba zasu bar shugaban ya fita ba har sai ya biyasu kudinsu.

‘Yan kasuwan sun bayyana cewa shugaban ya sanya su, su kawo musu man Gas Lita dubu 14 akan Kudi naira miliyan 4, a cewarsu, tun da suka kawo biyan kudin ya faskara.

Shugaban ‘yan kasuwan Alhaji Yusuf Kaura, ya bayyana cewa tun lokacin da suka kawo man Gas Hukumar (KAPWA) , shugaban Hukumar ya mayar da su kamar ‘yan maula lamarin da ya sanya su daukar matakin kwato hakkinsu.

Alhaji Yusuf, yace” yau kwana shida kenan da muka kawo Gas a nan amma sai yawo da hankali ake mana, ance muzo jiya Mu amsa kudinmu; munzo ance kudin an kulle a Save Mu bari sai yau, yau gashi munzo yaki ganinmu saboda haka muka rufe gate sai ya biyamu kudinmu”

“Hatta masu aiki a Hukumar basa jin dadin shugaban, Wanda suna daga cikin wadanda suka bamu shawarar rufe kofar” inji Kaura.

Lokacin da mukayi kokarin jin ta bakin shugaban Mista Martin, Wanda yake zaune cikin mota yana bugawa Waya, yace ” Ku barni pls! gama buga wayarshi ke da wuya sai motocin ‘yan sanda guda uku shake da ‘yan sanda da makamai wadanda sune suka bude kofar.

Tun zuwan Mista Martin, Hukumar aka fara samun matsaloli a cikin Hukumar mussan na rahin iya milki da Hulda da Jama’a.

Shima daraktan kamfanin da suka kawo Gas din Alhaji Mohammed Sani, yace” Mu ‘yan kasuwa ne ba maula ya kawo Mu ba saboda zamu tabbatar mun karbi kudin Mu naira miliyan 4 yau din nan saboda hakkin Mu ne”

Leave a comment