Rashin Biyan Kudin Wuta Ya Sa Muka Yanke Wutan Ofishin Gwamnan Zamfara …. Inji Hukumar PHCN

 

yari

Rahotanni daga jihar zamfara sun bayyana cewa rashin biyan kudin wutan lantarki da gwamnatin batayi ba, hukumar samar da wutan lantarki ta kasa (PHCN) sun yake wutan lantarki a gidan gwamnatin jihar dake Gusau.
Lamarin da ya mayar da fadar gwamnatin jihar zama cikin dinbim babu hasken wutan lantarki,
Rahotannin sun ruwaito cewa tun ranar larabar data gabat ne jamian hukumar samar da wutan lantarki suka yanke wutan gidan gwamnati bisa abin da suka kira rashin biyan kudin wuta da gwamnati bata iyawa, wanda hakan ya sanya suka yanke shawarar datse wutan gidan gwamnatin.
dama wannan bashi karo na farko da hukumar take kokawa dangane da rashin biyan kudin wuta daga gwamnati, hasalima, an ruwaito cewa hatta wasu daga cikin manyan jamian gwamnati basa iya biyan kudin wutan lantarki a gidajensu ba.
Haka kuma rahotannin sun tabbatar da cewa daukacin kafafen yada labarai mallakar gwamnatin jihar duk sun durkushe, kama daga gidan wallafa jarida Legacy da gidan rediyo da talabijin duk sun durkushe bisa rashin kula na gwamnati.
Haka kuma rahotannin sun tabbatar da cewa daukacin kafafen yada labarai mallakar gwamnatin jihar duk sun durkushe, kama daga gidan wallafa jarida Legacy da gidan rediyo da talabijin duk sun durkushe bisa rashin kula na gwamnati wanda rashin iya biyan wutan

zm

lantarki da nama maáikata duk suna daga cikin dalilan durkushewar su
Sai dai a wata ganawa da yayi da manema labarai a Gusau, jami”in hulda da jamaa na hukumar samar da wutan lantarki na jihar, Aminu Yakubu, yace sakacin gwamnati na rashin iya biyan kudin wata ya sanya suka yanke wutar gidan gwamnatin.
Yace tun shekarun baya gwamnatin jihar Zamfara bata iya biyan kudi wanda idan aka kawo mata takardar biyan kudin wutan sai tayi kunnen shegu da hukumar, a cewarsa, babu wata mafita da da zasu iya bi illa kawai su raba gidan gwamnatin da samun hasken wutan lantarki daga hannun hukumarsu.
Rahotannin baya bayan nan sun nuna cewa hukumar samar da hasken wutar lantarki tana bin gwamnatin jihar Zamfara bashin kudin wuta da suka naira miliyan 400
Wata majiya ta tsegunta mana cewa tuni dai yan majalisar dokokin jihar suka gayyaci wasu manyan jamián hukumar samar da wutan domin jin dfalilin da suka yanke wutar gidan gwamnati, inda majalisar tayi alkawarin cewa zata sanya baki a lamarin domin tabbatar da cewa an biya su bashin su.
Jamaá da dama suna ganin cewa dalilin da sanya gwamnati bata iya biyan kudin wuta shine gwamnan jihar baya zama a jihar ne, hasalima, duk wasu aikace-aikacensa yana su ne a tsakanin kaduna da Abuja.

Leave a comment