Sanata Shehu Sani Ya Karrama Nakasassun Kaduna A Majalisar Tarayya

A karon farko nakasassun jihar Kaduna sun kai ziyara a majalisar  tarayyar Nijeriya domin ganin irin gudummwar da wakilinsu yake bayarwa wajen kawo abubuwan ci gaban jihar Kaduna da kasa Baki data.

Nakasassun wadanda Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya gayyata, 

sun bayyana cewa a tarihin jihar kaduna wannan shine karo na farko da nakasassu suka ziyarci majalisar tarayya ta kasa inda suka ce bazasu manta da wannan karamci na shehu sani ba.

Nakasassun wadanda suka hada kurame guragu daga sassa na kananan hukumomi 7 a jihar kaduna, sun shigo cikin zauran majalisar be cikin murna da farin ciki suna kallon sama da kasa, wasunsu ma kamar zasu zubda yawu bisa yadda aka kawata ginin.

Da yake bayani a ofishinsa, Sanata Shehu Sani, ya bayyana cewa “lokacin da nake yakin neman zabe nace musu idan naci zabe zan kawo su ofis dina suga yadda muke aiki saboda sun zabe ni ne”

Nakasassun sun godewa wakilin nasu da cewa baya kyamarsu,acewarsu,zasu ci gaba da bashi goyon da dace domin ya ci gaba da zama wakilinsu har sai yace baya so.

Leave a comment