Hukumar NEPAD Ta  Jinjinawa Gwamna El-Rufa’i  Bisa Ci gaban Da Ya Kawo Jihar Kaduna


Hukumar tallafawa ci gaban kasashen Afrika (NEPAD) ta bayyana cewa jihar Kaduna tana daga cikin jihohi  a Nijeriya da aka samu ci gaba ta bangaran samawa matasa aikinyi da aikin Noma da Samar da hanyoyin da tallafawa mata domin bunkasa tattalin arzikin jihar.

Shugabar  hukumar (NEPAD)  a Nijeriya Madam Gloria Okobundu, ta bayyana cewa  sun gamsu da irin ci gana da aka samu a jihar Kaduna a karkashin jagorancin Nasiru Ahmed El-Rufa’i a cikin shekaru  biyu da yayi akan kujerar gwamnan jihar.

Shugabar ta bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki akan harkokin ci gaban al’umma, Wanda hukumar  NEPAD ta shirya a jihar Kaduna, inda tace hukumarsu tana kokarin ganin an samu ci gaba a harkokin Noma, sufuri, tallafawa matasa  maza da mata  ta hanyar samun dogaro da Kansu.

Madam Goria, ta ce kananan hukumomin suna da rawar takawa wajen tallafawa rayuwar al’umma, akan hakan tace zasu hada hannu da kananan hukumomin jihar Kaduna domin Samar da abubuwan ci gaban al’ummar su ta bangarori daban-daban  Wanda a cewarta kananan hukumomi sune suka fi kusa da al’umma.

Ta ci gaba da cewa an samu gagarumar ci gaba a jihar Kaduna musamman a yankunan kananan hukumomin jihar, tana mai fatan cewa gwamnan  zai ci gaba da namijin kokarin da yakeyi.

Acewarta, NEPAD, ita mai shiga tsakanice da manyan kasashe da ‘yan kasuwa masu zuba jari da gwamnatocin jihohi domin ci gaban tattalin arzikin kasa baki daya.

“NEPAD yana bin kasashe domin ganin ta tallafawa kasashe ta bangarori daban daban na ciyar da tattalin arzikin kasa hakan ya Santa kuka shigo jihar Kaduna domin ganawa da gwamnati da al’ummar jihar mugs hanyar da zamu bada tamu gudummawar domin bunkasar tattalin arzikin kasa ba alhakin yi ba aiki ne na hadaka”

“Kananan hukumomin suna da rawar takawa wajen ganin an tallafawa al’umma; wannan yana daga cikin dalilin zuwanmu Kaduna haka kuma munsa yadda gwamnatin jihar Kaduna take bakin kokarin ta na bunkasa harkar Noma da samawa matasa aikinyi da dai sauransu saboda zamu tabbatar mun baiwa gwamnan jihar Kaduna goyon bayan da ya kamata” inji ta.

A nasa jawabin sakataran gwamnatin jihar Kaduna  Wanda babban sakatare a ofishinsa Alhaji Abdullahi,ya godewa NEPAD bisa tunaninsu na shigowa jihar Kaduna da kuma bada hannu da gwamnatin jihar inda yace hakan zai taimaka wajen samun ci gaba. Yace gwamnatin jihar Kaduna tana maraba da masu son kawo ci gaba jihar, yana mai cewa NEPAD zata samu hadinka daga wurin gwamnati.

Leave a comment