Aikin Noma Da Ma’adanai Sune Mafitar ‘Yan Nijeriya…. Nuhu Bajoga

Tsohon mataimakin jihar Kaduna Ambasada Audu Nuhu Bajoga, ya bayyana cewa muddin ‘yan nijeriya suka rungumi aikin Noma da hakar ma’adanai sune mafitar halin rashin aikin yi da kuma dogaro da kai.

Audu Nuhu Bajoga, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai Jim kadan bayan kammala taron bajakolin Kayan ma’adanai na jihohin Arewa Wanda aka gudanar a Kaduna, inda yace baya ga Samar da aikinyi, hakar ma’adanai da Noma suna taimakawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasa.

Ya kara da cewa idan gwamnatocin Arewa suka rungumi aikin Noma Da hakar ma’adanai tattalin arzikin yankin Arewa zai kara bunkasa, hasalima, dogaro da man fetur zai zama tarihi.

Nuhu Bajoga  wanda jigo ne a fannin noma da ma’adanai, ya ci gaba da cewa” Allah ya albarkacin yankin Arewa da dinbim ma’adanai da kasar Noma amma duk anyi watsi da su an mayar da hankali akan man fetur Wanda hakan ya taimaka wajen jefa yankin cikin koma bayan tattalin arzikin kasa. Saboda haka mu rungumi aikin Noma Da ma’adanai  domin ci gaban tattalin arzikin yankin Arewa baki daya”

Akan hakan, Bajoga, ya bukaci matasa da rungumi aikin Noma Da ma’adanai Wanda yin hakan zai taimaka musu wajen ganin sun Dogara da Kansu ba tare da sun jira gwamnati ta tallafa musu ba.

Leave a comment