Babu Bako A Kungiyar IPMAN ….. Dan Sarki 

Dan takarar kujerar jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) shiyyar Kaduna Kwamarad Sanusi Bala Dan Sarki, ya jaddada cewa kungiyar su babu Bako a cikin ta sabanin yadda wani jigo a kungiyar yace baki sune ke kawo tarnaki a kungiyar inda yace babu Bako a IPMAN.

Bala Dan Sarki, ya bayyana cewa duk wani mutum da ya  mallaki Gidan man fetur a Kaduna kuma yake daukar man fetur a matatar mai ta Kaduna kuma  ya dauki ma’aikata ‘yan jihar ya wuce a kira shi Bako inda yace duk masu ikirarin cewa akwai Bako a kungiyar sune ke kawo tashin- tashina a kungiyar.

Sanusi Bala, wannda kuma shine Shugaban kamfanin hada-hadar  man fetur na Dan Sarki oil and Gas, ya bayyana haka ne ga manema labarai Jim kadan bayan kammala wani taron  sasantawa da kwamishinan ‘yan sandar jihar Kaduna yayi da jiga-jigan kungiyar ta IPMAN a ofishinsa.

Dan Sarki ,ya kara da cewa munafukai ne ke hana ci gaban kungiyar yana mai cewa” Zaman da akayi da kwamishinan yan sanda shi kadai ya Isa a samu Zaman Lafiya da kuma kawo karshen rikicin kungiyar da aka dade anayi amma abin mamaki sai ga wani ya tashi yana cewa wai baki sune matsalar mu Wanda irin sune matsalar kungiyar, mu babu Bako a kungiyar IPMAN”

Da yake magana akan kwamitin riko na kungiyar Wanda Alhaji Abdulfatah Murtala yake jagotanta, Dan Sarki, yayi watsi da kwamitin inda yace basu San wani kwamitin riko, hasalima, basu amince da kafa kwamitin Ba.

Leave a comment