Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Bada Shawarar Kara Kudin Man Fetur


Kwamitin kula da ayyuka a Majalisar Dattawan Nijeriya ya bukaci a kara farashin litar man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 150, inda za a yi amfani da kudaden domin zubawa a wani asusun gini da kuma gyara hanyoyi a  fadin kasar.

Sai dai shawarar kwamitin Ya zo ne shekara daya bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara kudin mai daga Naira 87 zuwa 145.

A jiya alhamis ne ya kamata Majalisar ta tattauna kan rahoton da wannan kwamiti da ke karkashin jagorancin Sanata Kabiru Gaya ya gabatar, to sai dai an dakatar da har zuwa wani lokaci da ba a bayyana ba nan gaba.

Kwamitin ya bayar da shawarar yin Karin Naira 5 akan kowace lita daya ta mai da kuma dizal da aka shigo da shi daga waje ko kuma wanda aka tace a cikin gida domin zubawa a asusun gyaran hanyoyi, kuma 12 daga cikin mambobin kwamitin 15 sun amince da matakin.ajeriya ya bukaci a kara farashin litar man fetur daga Naira 145 zuwa Naira 150, inda za a yi amfani da kudaden domin zubawa a wani asusun gini da kuma gyara hanyoyi a kasar.

Leave a comment