Gwamnatin Buhari Ta Kawo Zaman Lafiya A Arewa … Inji Jafar Maitama

Shugaban  kungiyar mawallafa jaridu da mujallu musulmai ta kasa (MMPAN) Malam Jafaru Maitama, ya bayyana cewa ko babu komai shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kawo Zaman Lafiya a Arewa duk kuwa  da  cewa gwamnatin tana fuskantar Kalubalen tattalin arzikin kasa.

Malam Jafaru, ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai Jim kadan bayan kammala taron Ramadan da  kungiyar  ta shirya wanda aka gudanar a dakin taro na Gidan Sardauna dake Kaduna inda yace gwamnatin Buhari ta samu nasarori a cikin shekaru Biyu ta bangarori daban-daban.

Shugaban ya bayyana takaicinsa dangane da yadde wasu ‘yan jarida suke wallafa wasu labarai da basu da Makama dangane da gwamnatin Buhari, inda yace gwamnatin Buhari tayi kokarin Kawo  Zaman Lafiya a Arewa Wanda ko wannan ya Isa a jinjinawa gwamnatin.

Akan hakan,shugaban ya bayyana cewa kungiyarsu tana bakin kokarin ta na hada kan ‘yan jarida musulmai dangane da muhimmancin Zaman Lafiya a fadin kasar nan baki daya.

Taron na baba mai taken “Samar da Zaman Lafiya da hadin kan ‘yan Nijeriya ;Gudummawar da ‘yan jarida  zasu bada”  ya samu halarcin manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar nan kama daga ‘yan siyasa, Malamain addinin islama da manyan ‘yan jarida.

Daga bisani kungiyar ta karrama wasu muhimman mutane da lambar yabo bisa kokarin su na KAaman Lafiya a kasar nan

Leave a comment